Offline

SHIN DAGASKE NE KWAYAR IDO ZATA IYA CIREWA A MAIDATA KUMA ACIGABA DA GANI DA IDON A LIKITANCE?? GA AMSA (GLOBE LUXATION..)

Abun da Malam bahaushe ke kira kwayar ido (eyeball), ba wai a rike yake gam a cikin kurmin ido (eye socket) ba kamar yanda mutane da yawa ke tunani. 

Akwai tsokoki (muscles), jijiyoyi da kuma wasu sauran ‘connective tissues’ da su ka rike kwayar idon, su ke ba shi damar juyawa daidai bukata (in all directions): sama da kasa, gefe da gefe, da sauran su. Shi kurmin ido (eye socket) wanda ya ke kasusuwa (bones) ne mabanbanta su ka hadu su ka samar da shi, babban amfanin sa shi ne bayar da kariya ga kwayar ido (eyeball) da kuma sauran ‘apparatus’ na gani (vision). 

A likitance, fitowa/zazzadowar kwayar ido (eyeball) daga cikin kurmin ido (eye socket) zuwa waje sanannen abu ne. Ana kiran shi da ‘globe avulsion/luxation’ (fincikewar/zazzadowar kwayar ido daga cikin kurmin da ke ba shi kariya). 

Sannan kuma, ficewar kwayar  idon ma hawa-hawa ne: akwai wanda kwayar ido zai saki (yana cikin kurmin ido, amma ya cire daga wani bangare na shi)- wannan bai da tsanani sosai (mild to moderate); akwai kuma mai tsanani (severe) wanda baki daya kwayar idon za ta fice daga cikin kurmin ido ta fito waje. Daga cikin su, na karshe (wanda kwayar ido zai fito baki daya) ne ba a cika samu sosai ba, har ma an rubuta takardun nazari da bincike (research papers) akan wasu ‘cases’ na faruwar shi da su ka zo da abun mamaki (ba zan kawo nan ba, amma akalla mutum na iya bincikawa ya gani). 

Sannan yanayin fitowar ma ya bambanta, idan kwayar ido ta fice baki daya, za ta iya bulluqowa waje kai tsaye (anteriorly), ko ta yi ciki wajen saitin hanci (nasally), ko kuma ta yi wajen kunci (temporally). Ko kuma ta yi wani wajen da ya hada sauran (of course akwai effect din gravity da zai ja shi zuwa kasa ko a wane direction ya fito, tunda yana reto ne a jikin wani abu da ya rike shi daga ciki). 

Jin ciwo (trauma) shi ne babban abun da ke kawo ficewar kwayar ido (traumatic globe luxation) wannan zai iya zama buguwar ido, dukan ido, cakewar ido, harbi da sauran su. Baya ga jin ciwo, akwai sauran cututtuka kamar ciwon dajin bayan kwayar ido (retrobulbar tumor), cututtukan rashin karfin ‘connective tissues’ kamar su Ehlers Danlos Syndrome, da sauran su; duk su na iya sanya kwayar idon mutum ya zazzado waje idan abu ya yi tsanani. 

Kuma idan ya faru, ana mayarwa ne a hade shi da abun da ya yi saura, bayan wani lokaci mutum zai dawo ya ci gaba da gani da idanun. Sai dai kuma idan a garin ficewar wani abu mai muhimmanci- misali jijiyar gani (optic nerve) ta samu matsala, ko wani abu makamancin haka; wannan ganin mutum ba zai dawo yanda ya kamata ba. 

To ban san me mutane ke yiwa izgili dangane da maganar Malam Zakzaky (H) na cewa an harbe shi, kwayar idon shi ta fita ta yi wajen kunci ya dawo da ita ba! Abu ne sananne, ya na nan a rubuce a litattafai, maqalu, kai har ma da takardun bincike da nazari na fannin likitancin ido. Ko me ya kawo karyatawa da izgili kuma? Jahilci, qiyayya, hassada, ta’assubanci ko kuma duka? 
Jahilci na rashin sanin girman Allah (T) da girman sha’anin Shi (kamar yanda na taba fadi kwanakin baya), da kuma jahilcin rashin sanin ilimin likitanci (amma mutane sun dage lallai sai sun yi izgili akan abun da ba su da Ilimi a kai). Aqalla dabi’ar dan Adam ne, idan abu ya saba da hankali, tunani ko sanin shi, kai tsaye zai karyata. A garin haka ma, wani lokacin mutum ayar Allah (T) ne zai karyata, ya yi ta izgili, kamar yanda aka yiwa wasu bayin Allah a tarihi. 

Wasu kuma tsantsar kiyayya da hassada ne ga Malam Zakzaky (H): su a wurin su me yasa Allah (T) Zai nuna ikon (ayar) Shi akan Malam Zakzaky (H) mutumin da ba su so? Me yasa Allah (T) Zai rayar da shi bayan an tabbatar musu an gama da shi? Me yasa Allah (T) Zai kula da al’amuran Malam Zakzaky (H) irin haka?! 

Ba a harbi Malam Zakzaky (H) a idanu ba? Aqalla akwai hoton shi da aka yi ta yadawa- cikin izgili har a kura (baro)- a baya dayan idon shi cike da jini, dayan kuma a kumbure. Sannan harbin bindiga ba zai iya cire kwayar ido ba? Mutum ya daina jahilci, ya je ya samu likitoci ya tambaye su. Idan kwayar ido ta fito shikenan ya zama wajibi mutum ya daina gani kwata-kwata? Aqalla idan mutum na da girman kan tambayar abun da ba shi da Ilimi akai ne ma, akwai ‘Google’ ai, mutum na iya bincikawa ya gani kafin ya zo yana nuna tsantsar jahilcin shi a fili. 
Amiral Mu’minin (as) ya yi gaskiya da ya ce: “dan Adam makiyin abun da ya jahilta ne”. Bisa dabi’a, shi zai karyata duk abun da ya sabawa sanin shi ne, Allah Ya kyauta. A wani gurin kuma, Amiral Mu’minin (as) ya ce: “Babu cutar da ta kai jahilci”. 

Duk inda jahilci da kiyayya su ka hadu kuwa, to sai dai Allah Ya kyauta kawai, babu bayanin da zai iya gamsar da wanda ya kamu da wadannan cututtukan na ruhi. Babu likitan da zai iya maganin su a kaf fadin duniyar nan. 

NB: Domin yanke uzuri ga masu neman gaskiya, hoton da ke kasa sakamakon ‘CT Scan’ ne da aka yiwa Shaikh Zakzaky (H) wanda ya nuna guragutsan harsashi (bullet fragments) makale a cikin kashin kurmin kwayar idon Malam (H), wanda ya ke tabbatar da gaske an harbe shi ba sau daya ba a idanun shi. Aqalla idan mutum na da ta’assubancin karyata masu daraja, don ya na ganin abun da su ka fada kamar wani ‘subjective evidence’ ne, aqalla mutum ba zai iya karyata hoton da ke kasa ba ko? Tunda shi ‘empirical evidence’ ne. Abun da ya rage kuma, mutum ya je bincika shin harbin bindiga zai jya cire kwayar ido baki daya ko ba zai iya cirewa ba?! 

Allah Ya kyauta. Allah Ya yi mana tsari da cutar jahilci, hassada da kiyayya. Ameen! 

- Najeeb Maigatari. 
08/04/2022

Post a Comment

Previous Post Next Post