Offline

Haƙika Har Yanzu Ƙasar Nan Tana Buƙatar System Irin Na Shaikh Usman Ɗan Fodio Ne.

—Baqeerul Uloum.

Matsalar da wannan Al'ummar take kai shi ne rashin System (Tsari) na adalci, Irin tsarin da Shaikh Usman Fodio ya tabbatar a wannan ƙasar kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka da Shekaru 100, Kafin zuwan Turawan Mulkin Mallaka Iyayen mu suna kan tsari (System) na addini Musulunci ne.

Wanda Shehu Usman Fodio yazo yayi tajadidi (Sabunta) Addini a wanchan Zamanin, kuma Allah ya bashi nasara akan sarakunan wanchan Zamanin nasa irin su Yumfa. Shaikh Usman Fodio yayi jahadi ne ta hanyar kira zuwa ga Musulunci, Al'umma ta ƴantu daga baƙin zalumci da danniyya na Sarakunan Gargajiya na wanchan Lokacin.

Shehu Usman Fodio ya kafa daular Musulunci wacce ta shafe tsawon Shekara 100 cur Musulunci ke iko da ƙasar nan, Al'umma ta tsaida Hukumci na Addini ta fatattaki zalumci da dan niyya na mugan sarakunan gargajiya.

Kunga ashe kafin zuwan Bature iyayen mu suna da ingantaccen System na addinin musulunci, Bayan Shekaru da jahadin Shehu Usman Fodio Turawan yamma suka zo suka ɗauke fuskar Addini daga gabashi suka mai dashi yammaci, suka zo ma da mutanen ƙasar nan wani System na daban!, Wanda ya saɓa da Addinin Musulunci.

Wanda kuma har zuwa yau Al'ummar ƙasar nan kan wannan gurbatacen System ɗin ne suke, wanda Baturen Ingilishi yazo dashi, tunda daga wanchan lokacin na zuwan Bature har zuwa yau Al'ummar ƙasar nan take ɓaganniyya da fama da zalumcin Turawan Yamma wanda suka ƙaƙaba mana!.

Har zuwa yanzu wannan tsarin da Turawan Mulkin Mallaka suka kawowa al'ummar musulmi ya kasa samarmana da mafita ta Duniya ma kawai balle ta lahirar matabbata, Don haka har yanzu Al'ummar nan tana buƙatar System Irin Na Shehu Usman Fodio na faɗa da zalumci da danniya!.

A faɗin ƙasar nan bansan wani Mutum, Sarki, Hakimi, Ɗan Siyasa, General, Kwamanis, Malami, wanda ya barranta da wannan System ɗin tun Shekaru 40 da suka gabata ba, in ba (Shaikh Ibraheem Zakzaky) ba!, idan kuma akwai wani Mutum wanda ya shelanta haka to kuzu mu bi shi!, Idan kuma babu wannan Mutumin daya Shelanta ta waye ga wannan System ɗin to Kuzu mu bi Bayan Malam Zakzaky [H].

—Baqeerul Uloum.

Post a Comment

Previous Post Next Post