Offline

ANA KOKARIN HADDASA RIGIMA TSAKANIN HAUSAWA DA FULANI

To yanzu hanyoyin cimma isar da sako lokacinsa ne sosai, tunda yanzu kamar yadda nace an bude idanun mutane. Yanzu kamar yadda nake cewa shi Mazlumiyyar da aka mana har yanzu mutane sun kasa jingina abin da ke faruwa da wannan abin da aka aikata, kuma shine dalili ba wani abu ba. Dama ana zaluntar mutane da kashe-kashen nan, saboda su masu yin suna kashe-kashen kare-dangi ne. 

To na ga wani abu da yake gudana yanzu, wanda ina ganinsa a rubucee-rubuce da maganganu da ake yi a Facebook, na farko yadda ake kokarin a hada fada tsakanin bangaren al’umma da wasu su kashe juna. 

Fulani makiyaya, wadanda su an san su, shanun nan sune rayuwarsu, suna tafiya lafiya lau daga waje zuwa waje suna kiwonsu, ba a taba samun matsala shekara daruruwa tare da su ba, su kiwonsu suke yi, shanun sune rayuwarsu, in kaka ta yi manoma na marhaban da su ne, su zo su sauka a gonakinsu don su sama musu taki, da safe su je kiwonsu matansu su kawo nono gari, haka ake zaune shekara da shekaru lafiya lau.

To, yau an je an dira a kansu an raba su da shanun, an zauta su, an basu kuma bindigogi. Cikin irin zauta Fulanin da aka yi, akwai wani wanda aka je rigarsu aka kada shanun, sai kuma aka kwashe matansu, har ma in suka ga tsohuwa ce za su iya kyale ta, amma suka ga wata yarinya tana goyo, sai suka fizge goyon, suka ce wa mijinta wannan danka ne? Yace eh. Suka fincike shi suka wurga masa dan ya café, suka tafi da matar. Irin wannan in mutum ya haukace meye ba zai iya yi ba? to sai kuma a bashi bindiga. Bayan an zauta mutum sai a bashi bindiga.

To, ana nan sai aka ce an samar da ‘yan Ta’adda, wai Fulani ne, kashe-kashen nan sai a ce Fulani ne suke yi. Wai Fulani ne suke kashe-kashe, alhali in da akwai wani mutum da ya fi kowa zaman lafiya, ba kamar Bafullatani.

Na’am, na san akwai wasu makiyaya da suke zuwa daga can Arewan wajen Nijar, wanda su dabi’arsu wani iri ne, wadanda ake ce musu Bafolo, in ka ji an yi rigima da manoma to su ne, amma banda Fulaninmu da dama ake zaune da su, ba su rigima tsakaninsu da manoma. Tsakaninsu da manoma zumunci ne. To yanzu sai aka zo, makiyayi Bafullatani an raba shi da Saniya an bashi bindiga, dama shi bai san komai ba saniyar it ace rayuwarsa, to an ce masa yanzu sunansa Dan Ta’adda. 

To bayan wani lokaci yanzu sai ana so a kawwana ‘yan Ta’adda Hausawa, su kuma su rama a kan Bafullatani. Wannan abu da ban al’ajabi. Ka ji wadansu suna maganganu su kuma wai su Hausawa ne, suna zagin Fulani. Nace o’o! wannan abu ya bani mamaki.

Shekarun baya kamar shekara 22 kenan na tafi Afirka ta Kudu, ina magana, a cikin maganata a kan rigimar da aka yi tsakanin Hutu da Tutsu a Ruwanda da Burundi, sai nake cewa dalilin da yasa ake wannan rigimar na Kabilanci tsakaninsu saboda su  a Musulmi bane, shi Musulunci yana hada mutane su zama abu guda. Sai nace mu a Nijeriya akwai Hausawa da Fulani, to nake cewa yadda Hausawa da Fulani suka dunkule suka zama abu daya a matsayin ‘yan addinin Musulunci ko Shaidan ya yi kadan ya hada fada tsakanin Bahaushe da Bafullatani.

Domin sai ka rasa ma waye ma Bahaushe tukunna, don kowa sai ka ga shima Hausawan ne kawai don suna magana da Hausa, kuma in Fulani jini ne, ko ina akwai jininsu, ba inda babu jinin Bafullatani a ko ina, tunda banda makiyaya, akwai kuma wadanda ake ce ma Fulanin gida, to in ka je gida din za ka ga an cakude ne. Ni ban san ta yadda za a yi a raba ace wannan Bahaushe ne, wannan Bafulatani ne ba, ba ma zai yiwu ba. Nake cewa ko shaidan ba zai iya hada fada tsakaninsu ba. 

To sai daga bayan da na yi wannan maganar, sai aka ce ai lokacin da ake rigima tsakanin Tutsu da Hutu akwai unguwannin Musulmi, su basu yi rigimar ba, da Hutun da Tutsun sun zama guda. Nace kai da na san wannan ma da na fada, domin shi Musulunci ya kan dinke mutane ne su zama abu guda, wanda yake wani addini baya yi.

Don akwai wani Bahute wanda yake Pasto ne, ya tattara Tutsawa a cocinsa don ya basu kariya, sai ya je ya kira masu kisa suka zo suka far musu suka karkashe, suka kuma kona cocin tare da su a ciki, suka kona cocin kurmus tare da mutane. To har wani yake cewa shi baya ma kaunar ya ga coci, saboda irin wannan abin, don a coci aka kona su. Bahute ne ya tara Tutsawa ya basu kariya a coci, sai ya kira masu kisa aka ritsa da su ba wanda ya sha. 

Wata mata tana ba da labari, ni na ganta a Talabijin tana ba da labari, tace da aka sari na kusa da ita sai ta rungume ta suka fadi, sai ta yi shiru, to sai suka zo suna bi daya bayan daya, sai taji wani yace wannan abin yana numfashi, wannan abin. Kun san in aka ce wannan abin ana nufin ba ma bil-adama ba kenan. To yana cewa wannan abin yana numfashi, sai ya je ya dauko wani katon guduma ya buga mata a ka. 

Daga nan bata sake sanin inda take ba, farkawar da za ta yi sai ta ji wadansu abubuwa suna ta binta, sun mamaye jikinta tana karkadewa, sai ta ga ashe tsutsotsi ne, duk wadannan da suke kusa da ita duk sun rube, tana cikin rubabbun gawarwaki, har tsutsotsi sun kewaye ko ina. Tace sai wani manomi ya ganta ya ja ta ya kai ta gidansa, aka wanke ta aka boye ta.

To ka rasa mene ne dalilin rigimar tsakanin Hutu da Tutsu, sun kitsa musu mummunan gaba a tsakaninsu, kuma Turawa na da hannu a ciki. Na san akwai wata ‘yar International Committee of Red Cross da suka kawo min ziyara, sai nake ce mata ai rigimar Hutu da Tutsun nan ai ku Turawa ne kuka haddasa, su Amerika suna bayan Hutu, Faransa tana bayan Tutsu. Sai tace ‘unfortunetly than is the truth’. 

Wannan irin haddasa rigima da suka yi, da wani irin muguwar gaba, an ce da wani dan Hutu da uwarsa Tutsu ce, ya kashe ta shi da kansa, yace kuma ko sau nawa ta dawo duniyar nan zai kashe ta. Nace tir! Wannan irin al’amari. 

To haka suka je suka haddasa na Kudancin Sudan tsakanin kabilun Dinka da Non, suma sai ka ga mutum kanjamamme kashin awazansa a bayyane, bai da burodi, yana zaune a rumfar ciyawa, amma yana da bindiga A.K da jigidan harsasai, bindigar nan in abin a sayar da ita a kasuwa ne za ta saya masa abincin da zai yi watanni yana ci, amma yanzu yana fama da yunwa kuma yana da bindiga. To tambaya, ya za a yi mutumin da yake fama da wannan talaucin zai samu wadannan bindigogi masu tsada? Ina bindigogin nan suke fitowa? 

Mu ma sai aka ce gashi an zo mana da shi, an ba Bafullatani yanzu kuma ana ba Bahaushe. Yanzu zage-zage ake yi, in ka ji zage-zagen da wasu suke yin a fitan arziki da sunan su Hausawa ne; wai su Fulani sun zo nan ne basu da kaza, har da zagin Shehu Usman Danfodiye, har da babansa. Na ji wani wai shi Dan Hausa Sudani, yana ta surutu, suna ta zage-zage wai su Hausawa ne, kuma suna zagin Fulani ne. 

Sai kuma aka samu wasu Fulanin suma suna zagin Hausawa; wai ai mun same ku maguzawa ne, mu muka koya muku addinin Musulunci, kuna tafiya tsirara mu muka koya muku riga. Duk maganganun nasu ba mai gaskiya a cikinsu. Zage-zage kawai ake yi.

To sai nace to ina ganin bayan sun kauwana ‘yan ta’addan Fulani, za su kuma kauwana ‘yan ta’addan Hausawa, sai ku kashe kanku. To, yana da kyau ya zama an fadakar da mutane wannan hadarin da ake son kawowa. In kun kashe kanku, su wadancan suna da asara ne? Dama suna so su rage yawanku, illa iyaka su baku makamai su ingiza muku kiyayya ku karata ku kashe kanku.

Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
www.cibiyarwallafa.org

Post a Comment

Previous Post Next Post