To, abin da nake cewa, tunda dai jarabawa ce, jarabawa ga kowa da kowa, an jaraba mu. Dama in kace tafarkin Allah, jarabawa na nan tafe. To, mun ga jarabawa, kamar yadda Allah Ta’ala yake cewa ga Muminai bayan karon Uhudu; “Walaqad kuntum tamannaunal mauta min qabli an talqauhu faqad ra’aitumuhu wa antum tanzurun.” (Ali-Imran: 143).
Da can kuna burin mutuwa, ka san ana karanta ladar shahidi, mutum zai ce ina ma nima na samu shahadar nan. In kun tuna wata magana da nake fadawa ‘yan Kano nake cewa ranar Yaumu Shuhada na karanto wani yanki na wani dogon Hadisi da yake cewa ranar Alkiyama za a ba Shahidi ceton danginsa dubu saba’in. Kun san akwai hadisin da yake cewa ko mutum saba’in a dangin uwa, saba’in a dangin uba. To, wannan kuwa sai yace dubu saba’in, ba saba’in kawai ba.
Aka ce za ka ga kowa yana kokawar ace yana da dangantaka da wannan, har ma wani yace ai na fi ka kusa da shi. Ana ba da misali da wannan, wani zai ce ai kakanmu daya ne. Sai wani yace ai ni kuma a gidanmu ya samu mata. Kowa yana kokarin yace shi kusa yake da Shahidin, don ya samu ya tsira. Mutum dubu saba’in. Ka ga in ka ji wannan Malam, sai kace ina ma kaima ka zama Shahidin nan ne.
Ko ka ji an ce Aljanna babu hisabi. Sai ka ga kowane yana so ya zama Shahidi. To, amma kuma wata rana na nan zuwa da za a gwada a ga ko da gaske ne.
Alhamdulillah, mun godewa Allah. Mun godewa Allah, an samu gwaraza da suka dake, suka fuskanci mutuwa ‘ra’ayal aini’, suka fuskanceta gadan-gadan ba ja baya. Wannan ko ka ki mu sai kace an yi haka nan. Ko makiyanmu sun san an yi hakan. Kuma mun san cewa wannan karfin imani ne.
AKWAI MASU KEKESASSUN ZUKATA:
Amma na san har yanzu akwai masu kekesassun zuciya, da suke cewa wai ana kawo kudi (daga waje). Nace ‘ajieeb!’, ni dai da ma ka ce mana mu mahaukata ne da ya fi, ya fi in ka ce mutum mahaukaci ne, in ya ga wuta sai ya je ya fada tunda ba shi da hankali. To amma kace wai ana bashi kudi? To ina amfanin kudin (da aka bashi din) bayan ya mutu?
Yanzu kai mai cewa ana ba da kudi nawa za a baka kai ka je ka fuskanci mutuwa? Da ka ce ai wadannan mahaukata ne, sai nace eh gara haka nan, amma ba kace kudi ba. Don aikin da ake yi in mutum yana bukatar kudi don ya yi amfani da kudin ne ko?
Amma yanzu akwai kuma wasu masu kekesassun zuciya su kuma abin duniya suke kallo har yanzu, su kan ta surutu dangane da abin duniya. Nace to shikenan, dama Allah Ta’ala yace, ba idanuwa ke mutuwa ba, zukatan da ke kiraza ne. Idan mutum zuciyarsa bata gani, to idonsa me zai kalla? Zai rika kallon-garau (kamar yana gani amma baya gani) ne, ya rika ce kun ga wancan motar katuwa, ka ga babban riga, naga ma kiba yake fa. To, idonsa yake gani, amma zuciyar ta kekeshe, domin ba a ganin imani da ido.
Kuma ba a ganin Ikhlasi, wannan ba zai ganshi ba. Amma da zuciya za ka iya ganin Imani, za ka iya ganin Ikhlasi, za ka iya ganin sadaukarwa. Su ma kila su ga sadaukarwar, basu so su gani ne.
SHAHIDANMU SUN CI JARABAWA:
To, Alhamdulillahi wasu sun cika alkawarinsu sun kuma ci jarabawa, sune Shahidanmu, wadanda suka tsaya tsayin daka, suka fuskanci mutuwa ba tare da ja baya ba. wadannan muna alfahari da su, kuma muna fatan Allah ya sa su zama masu taimakawa Qa’im (AS), ya dawo da su a ‘Rij’a’ su rayu wanda su kuma ba za su sake Shahada ba.
Don in mutum ya yi shahada, in ya dawo ba Shahada zai sake yi ba, zai rayu ne komai gumurzu zai fita, sai dai yam utu a karshen ajalinsa. Allah ya sa su dawo su rayu, musamman ma irin matasan nan, da yara kanana, Allah ya basu wata damar ta biyu Insha Allahu.
Sannan kuma akwai wadanda aka ji ma rauni daban-daban wadanda har yanzu suna fama da raunuka daban-daban da rashin lafiya. Allah Ya kambama lada gaba daya, ya kara dauriya kuma ya ba da lafiya.
Sannan sai kuma su wadanda muke jajanta ma wa, Allah Ya kambama lada. A yi ta addu’a, insha Allah. Har nake cewa shi duk lokacin da ka tuna da Shahidi, ka zubar da hawaye ko ka ji wani abu a zuciyarka, to karin lada ne. kuma lallai za mu rika tuna su, mun dinga tuna su kenan. Wannan waki’ar ba mantawa da ita za a yi ba, za ta shiga kundin tarihi insha Allahu har abada.
WADANDA SUKA YI KASHE-KASHE SUN GA JAZA’I:
To, da yake mun ce jarabawa ce, su ma Mahukuntan fa an jaraba su, da ma ma’aikatan. Kai! Na ga kekesar zuciya. Sannan kuma ban san ko suna koyon darasi ba, don kun san da yawansu sun mace? Da yawan wadanda suka yi ta’asar nan, da yawa sun mutu. Allah Ta’ala ya bar manya-manyan sunan nan suna gani, ya kyale su su gani, amma su kananan da yawa duk sun tattafi.
Da (wasu) manya ma, don akwai Janarorin da suka tafi, akwai Janarori da yawa da suka tattafi. Akwai wani da yake fada min tun muna tsare a nan Abuja ya kawo min ziyara yake ce min, wani Kanal yake ce masa shi ya san ya kusa mutuwa. Sai yace me yasa kake cewa haka? Sai yace shine ya jagoranci ‘attack’ a Darur Rahma. Yace kuma wadanda suka raka shi su biyu, Major da Kaftin duk sun mutu. To kuma kwanan nan sai muka ji an ce shima ya sheka Barzahu, amma ya zama Birgediya Janar, amma ya sheka Barzahu shima.
Da labarurruka daban-daban da za ku rika ji masu ban al’ajabi. Akwai wani da aka ce shi Commander dinsa yace mutum nawa ka kashe? Yace mutum 51. Yace kai ka kashe da yawa, to zauna ka huta, ya zauna. Sai rannan su sojojin da kansu suke fadi, sai gashi sun fita irin rawar dajin nan suna dawowa a nan Zariya, sai motarsu ta arce ta bar hanya ta shiga daji, to shi sai ya diro.
Da ya diro sai motar ta rika kafarsa ta rika jan kansa, ta je ta tsaya sai ta kama da wuta. Su sauran sojojin sai suka fiffita, amma shi daga baya sai aka ga konannen gawarsa. Ya kone kurmus, aka ga gawayinsa. Amma sai aka ga ashe motar da take janshi ta tsinke kan, sai aka tsinci kan, sai aka gane ashe wane ne. Shine wanda yace ya kashe mutum 51. To, an yi jana’izar kan da raguwar gawayin. Labarurruka da yawa.
Akwai kuma wani wanda ya je gidan shan shayi, a irin teburin shan shayi din nan, sai yana ce musu ai da shi aka yi ‘operation’ din Zariya, yace shi kai kawai yake harbi, duk wanda ya harbe shi a ka ya harba. Sai mutanen da ke wajen suka ce, to kai ba ka ji wani abu ba? Yace to me zan ji?
To, da ya gama shan shayinsa ya tafi zai tsallaka titi, sai suka ji fas! Wata Tifa ta wuce, suka ji kara, kawai da suka zo sai suka ga shine kansa ya baje a kwalta, babu kan. Hannunsa lafiya lau har da agogonsa. Suka uhm, yanzu yake cewa shi kawai kai ya rika kashewa, gashi nan ba kan. Tifa ta bi ta kan kan ta fasa, ta niqe a kan kwalta. Sai ya zama duk jikinsa lafiya lau amma babu kai.
To, labarurruka irin wannan daban-daban wadanda aka ji na abubuwan da ya sassamesu. Nace suna ganewa kuwa? Akwai wani jami’in tsaro da yace suna ganewa mana.
Akwai wani a nan bayan harbin Arba’in kuma na nan Abuja, shima aka kai wani mutum asibitin Federal Medical Center da ke Keffi, gaban akwai ‘yan uwan da aka jijjima ciwo suna kwance a wannan asibitin, shima sai suka ga an kawo wani mutum duk jikinsa da bandeji, aka kwantar da shi a inda suke.
To suna nan sai mutumin ya ga wasu sistoci da Hijabai suna zazzaune, sai ya tambaye su, ku Shi’a ne? Suka ce eh. Sai yace to ku yafe min, mu ne muka yi ‘operation’ din nan. Yace bayan abin da muka yi wasu mutum uku daga cikinmu da direba suna mota, sai suka yi hadari, amma shi direban ba soja bane, amma sauran sojoji ne wadanda kuma da su aka yi ‘operation’ din, sai motar ta kama da wuta duk suka kone, shi kadai direban ya fita, tun daga nan muka fara tunanin sakamakon abin da muka yi ne.
Yace, ni kuma bayan da muka yi abin da muka yi aka bamu kudi, sai na sayi sabuwar babur, na je na sha mai. To ya hau babur din, sai ya lura Mai din na zuba daga tanki, sai ya duka yana so ya toshe bakin, sai babur din ya fadi ya kama da wuta, sai babur din ya kone kurmus, shi kuma ya kona shi. Shine aka kawo shi asibitin nan. Shine yake cewa yan uwa su yafe masa. To, bayan ya kwana daya zuwa biyu shikenan shima dai ya mutu.
Nake cewa irin wadannan ya faru da su da yawan gaske, haka nan suka yi ta mutuwa. Har ma wani yake ce min a nan 1 Div. da ke kaduna, wata mata take cewa wai ba a mutuwar Allah da Annabi ne a barikin nan? Da zaran wani ya mutu sai a ce ya je Zariya ‘operation’, duk wanda yam utu sai a ce ya je Zariya. Tace wai ba a mutuwar Allah da Annabi ne a barikin nan?
To haka nan, suma manyan haka ne. Kuma manya-manyan suna gani amma su basu damu ba, suma wadanda suka saka su, iyayen gijinsu basu damu ba, in duk za ku halaka gaba dayansu ba ya dame su bane. In ma suna iyawa za su halaka ku gaba daya, saboda su bukatarsu shine ya zama ma babu ku. Dukiyar da ke karkashin kafafunku ne suke bukata ba ku ba. Su magidantan da suka saka su suna iya yin wannan. Ala ayyi halin, abin da nake cewa shine suma wadanda aka saka su aikin an jaraba su.
JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) GA IYALAN SHAHIDAI RUKUNI NA BIYU A RANAR 5/12/2021 (3)
Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
www.cibiyarwallafa.org
Tags
Jawaban Jagora