Zainab na daga cikin misalin yara wadanda suka samu kansu cikin tashin hankali a Nigeria.
Gwamnatin Nigeria ta rattaba hannu akan dokar 'yancin yara a shekarar 2003 a lokacin mulkin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo. wannan yasa muke saran kare yara akan kowace barazana da kuma magance take hakkokinsu.
Saidai munga sabanin hakan tayadda Jami'an tsaron Nigeria suka dira akan 'yan uwa Musulmi na harkar musulinci a Nigeria karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (h) agarin Zaria a Shekarar 2015.
Inda aka kashe akalla yara 200 yayin kisan kiyashin na zaria.dukda haka wanda suka kubuta daga mutuwa basu tsiraba domin wannan harin ta'addancin yajefasu cikin wani mummunan yanayi.
Yar shekara 8 kacal yayinda kisan kiyashin ya faru , Nargis Abdullahi "tace tasamu azabtarwa daga hannun sojoji, kafin wannan waki'a ta 2015 dama ta samu raunuka a wasu waki'o'i shekarun baya.
"Ganin yanda aka rinka kashe mutane gabana shine abinda yafi muni a abinda yataba faruwa dani, naga akalla mutum 10 wanda suka rasa rayuwarsu a yammacin na ranar asabar, 12 ga December, yara da mata da suka rabu da mazajensu.
Na samu kaina cikin gallazawa tare da wasu yara dayawa sa'annina, a yammacin lahadi, wani Soja ya tambayeni ina mamata take, kafin na mayar masu amsa, wani soja ya mari fuskata da hannayensa guda biyu, wanda yasa na dainaji na tsawon awa 2.
Daga baya sun kwashemu zuwa barikin sojoji inda naga daruruwan mata, ciki harda mamana daure da igiya kamar yar ta'adda.
"Ganin mamata cikin wannan muzgunawa yasani cikin damuwa, akwai sama da mata 300, da aka kama,
Sojojin sunyi kokarin kashemu yayinda suka daukemu zuwa Police criminal investigative na kaduna"
Mun kasance a tsare a hannun 'yan Sanda na tsawon kwana biyar
Kuma Lokacin sanyine, nakasance ina kwana a hijabin mamana, yan sandan sun azabtardamu da tambayarmu suna cewa mu fada masu mundaina harkar musulunci.
© Freedom Fighters Ng.
Aciki akwai wani bangare na Rahoton Humangle.
By Mahadi Tukur & Al'ameen
Tags
Zaria Massacre