To wannan al’amari ni sai na lura, ainihin fa a mai da Bafullatani abin a kai ma hari yana da wata manufa, suna da wata manufa a wajen kau da Fulani ‘kususan’. Na farko dukiyar da suke so su diba a dazuzzukan nan su makiyayan nan suna keta dazuzzukan, suna son kar a gansu.
Akwai wani abu da aka yi a Iran, lokaci Shah da Turawan Ingila suna so su su bi da bututun Mai, to sai suka ce a hana makiyaya. Suna da wasu makiyaya wadanda sun yi kama da makiyayanmu na nan. Akwai wata Kabila ana ce musu Bakhtiyal, sun yi kama da makiyayanmu na nan. Yanzu zamanin Talabijin za ka ga ana yin ‘documentary’ a kansu.
Da yake suna da gatanci su makiyayan Iran, har akwai mai ba shugaban kasa shawara kan makiyaya. Su ana binsu ne da makaranta da asibiti, duk inda suka sauka nan za a ya da zango, ba a ce musu su tashi. A yanzu kenan fa da aka yi ‘revolution’ a karkashin Jamhuriyar Musulunci, amma a lokacin Shah akwai lokacin da Turawa suka sa aka hana su motsi.
Su kuma idan suka zauna a waje, in ciyawan wajen ya kare suna yin gaba ne, sai ya zama aka takura su aka hana su motsi. To, sai na ga kamar shigen irin wannan ne, mu kuma a nan Turawan da suka zo abin da suke so shine a kawar da Bafullatani ne, ya zama bashi ne sam-sam, saboda su malala bututun Mai shi ya zama ba shi.
To kuma ko ba komai suna shirin in sun haddasa rigimar da ya kau da Bafullatani, to kuma za su koma kan wanda ba Bafullatanin ba. don kowa da kowa ne. Yanzu kauyukan da manoma ke zaune, suma ana zuwa a kai musu hari a kokkona ace Mahara ne, su ba a ce musu Fulani bane, an ce wannan mahara ne, su je su kona gidajensu da rumbunansu, babu noma kenan. Sannan a bi makiyaya suma a harbe su a kwashe dabbobin. Ba noma kenan ba kiwo.
To, in ya zama ba noma ba kiwo, to su wadanda suka dogara da noma da kiwo me za su yi? Dole za su watse daga kauyuka su shiga gari, in sun shiga gari me za su yi? Ku fada min? Ai sai bara. To me za ka yi? An kona maka gidanka da komai naka, baka da komai, kuma dama abin da ka sani kai manomi ne ko ka iya kiwo ne, kai ba ka iya kira ne ko wani abu bane, ko wani aiki aka baka za ka sha wahala ne kawai tun baka iya ba, in an ce ka yi gini baka iya gini ba ana neman a yamutsa rayuwar mutane ne. Kuma abin da ke faruwa kenan.
ANA SHIRIN HADA FULANI DA HAUSAWA FADA:
To, kususan batun Fulani da ake yi yanzu, kwanakin baya na yi wata magana lokacin da Cibiyar Wallafa suka zo nan, Mawallafa da Mawaka, na yi wata magana dangane da abin da na gani yake gudana a kafofin sadarwa din nan, akwai wani ‘site’ wai shi Fulde Hande, to kamar abin kirki ina bin wannan Fulde Hande din, shafi ne a Facebook.
To, ina bin (shafin) sai kawai na ga ana zagin Fulani, wai Fulani basu da asali, Fulani dama sun zo ne suna kiwo basu ma da riga, Bahaushe ya basu riga. Nace ha’a! me ya kawo wannan magana kuma? Kai ka taba ganin shafin Fulde ana zagin Fulde? Nace wannan wane irin abu ne haka? Sai can kuma sai aka fara zagin Hausawa; ku kuma dama Hausawa Maguzawa ne, mu muka kawo muku addini.
To sai nace toh, na fahimta. Wannan Fulde Hande din nan makiya ne suka kirkiro shi. Yanzu zage-zage ne kawai na fitan arziki, wannan na zagi da sunan shi Bafullatani ne yana zagin Hausawa, wannan yana zagi da sunan shi Bahaushe ne yana zagin Fulani. Kun ga wato kenan yanzu ana so a haddasa wani fadan, mai yiwuwa a samar da wasu ‘yan ta’adda da sunan su Hausawa ne, ko kuma a fito da wasu ‘yan ta’adda da sunan su kuma Fulani ne, sai a yi ta gwabzawa.
Wannan tsararren abu ne na kitsa rigingimu daban-daban wanda zai karata a kan al’umma ne, amma musamman al’ummar Fulani. Saboda su akwai su da wata manufa ta ganin an kawar da Fulani, musamman makiyaya din nan, ko kuma a gurgunta su. Amma wannan in sun yi shi zai shafi kowa da kowa ne, ba wanda ba zai shafa ba, al’ummar gaba daya zai shafa, kuma dama abin da suke bukata kenan.
FULANI SU YI HATTARA DA TARKON DA AKA DANA MUSU:
Kuma in aka lura duk wadannan abubuwan da ake yi ana yi ne ga al’ummar Arewacin kasar nan ko ma a ina suke, da kuma al’ummar Musulmi ‘khasatan’, to amma abin sai ya fi tsanani a kan su kansu Fulani din.
Nake cewa a yi hattara, a yi hattara. Na san in aka maka tarko, ka gane kuma tarko ne aka yi, kauce masa za ka yi ba za ka fada masa bane. Alal misali, ga tarko an sa, amma in ka saka kafarka zai rike ka, ka san kaucewa za ka yi. Ko dabbobin daji su kan gane tarko, suna kauce masa. Har bera ma yana gane tarko, in ya gane sai ya kauce.
To saboda haka tunda an ma Fulani tarko, na farko an karkashe su, an kwashe shanunsu, sannan sai kuma aka zo aka ce musu ga mafita, aka basu bindiga, ana koya musu yadda za su yi harbi. Sai kuma su kuma suka je suna ramuwar gayya, a kan wasu mutane. To ka ga sun fada tarko. Saboda haka akwai bukatar ko da an zalunceka kai kuma kar ka yi zalunci. Tunda ba a magance zalunci da wani zaluncin.
Abin da nake cewa, in wani yai maka laifi, kamar yadda suke ma Fulani ‘jamma’i’ (hukuncin gaba daya), in an ga Bafullatani kawai sai a far masa a matsayin shi Bafullatani ne. Ace saboda mene? Ace saboda wasu Fulani sun kawo hari. Saboda haka Bafullatani yana tafiya a kan hanya, ba abin da ya shafe shi, bai san hawa ba bai san sauka ba, sai a dira masa a yi ramuwar gayya a kansa. To, shima ba sai ya yi ramuwar gayya irin wannan ba, shima ya dauki bindiga shima yace zai rama ba, sai ya zama ainihin bukatar makiya ya biya, na cewa yanzu to ku kashe kanku.
Dama bukatar makiyan kenan, ku kashe kanku, kun mana yaki. Ba sai mun zo mun yake ku ba, mun baku bindigogi, wannan mun bashi bindiga ya kashe wannan, wannan mun bashi bindiga ya kashe wannan. To, amma idan ya zamana daya ya kauce, wanda na san kaucewa wannan yana da wahala, tunda yake musamman kana raye ne ana binka har gida, kamar yadda mu aka yi mana da sunan an ce mu Shi’a ne. Aka bi mu aka ce kashewa za a yi. To, amma an ga cewa mu ba mu mai da martani ba. Ba a iya ingiza mu ba.
A wancan karon bayan da na fito (daga kurkuku) bayan waki’ar Abacha, na san wani Dan BBC ya tambaye ni. Nace to duk abin da za su yi har abada ba za su iya harzukamu su ga cewa muma mun shiga mai da martani da kashe-kashe ba. Kuma basu ga wannan daga garemu ba, ko mutum ya ki mu, ya san bamu mai da martani ba. Kuma ya san za mu iya idan muna so.
Sun so ma su kauwana wasu da sunan mu ne, su yi barna su ce mu ne, amma ya gagara. Saboda su da kansu ma su kan ce ko an yi za a ce karya ne. Sun sha kokarin su kama wadansu mutane sai su nemi su kala musu laifi, su ce wai ko an gansu da bindigogi. Akwai wadanda suka nemi su kama, har ma akwai wadanda suka kama din ma a nan Abuja, suka yi musu hoto, suka sa su rike jar tutar Ya Husain a baya, sai suka jera bindigogi kuma a gabansu, suka ce gasu nan an kama su ne, kuma suka kai kotu. Amma duk da haka kotu ta kori karar ta kuma sallami mutane. Duk abin da ka fada dangane da ‘yan uwa, ka nemi ka kala musu sun yi wani laifi, za a ce karya ne. Saboda basu yi din ba, basu taba tunanin kuma su yi ba.
To, irin wannan ya kamata ya zama, matakin kenan, sai ya zama in kai baka mai da martanin ba Allah zai maida maka, in baka rama ba, Allah zai rama maka. Don Allah ba azzalumin kowa bane.
Iyakar iyawarmu ya kamata mu yi kokarin mu kaucewa a ce Fulani suma an jingina musu ko ‘Kidnapping’ ko hare-hare na bindiga. In ma wani ne zai yi, ya zama shine amma ba da sunan Bafullatani ba. Yauwa. To, na san wannan yana da wahala. Dauriya na da wahala, amma dauriyar ne magani, har Allah ya kawo mana mafita.
MAFITA SHINE MU KOMA GA ALLAH DA ADDU’A:
To kuma iyakar iyawa na san tunda ko tafiya ma yanzu kana tafiya kai Bafullatani ne kana cikin hatsari, ballantana ace za ka kora shanu, misali kace za ka bar kasar nan da shanunka, ta ina za ka bi? Duk inda za ka je za ka tafi da shanunka ne. Sai dai daidai gwargwado kuma in ka samu kafar da za ka iya fita, abin da ya kamata kenan. Sai ka bar musu wajen da suke kai harin, ka je inda kake tsammanin aminci.
Amma na ji an ce ana bin mutane har ma inda suka gudu suka je, ana binsu har can inda suka je a kama su a kashe. To wannan dai yanzu bamu da wani mafita illa mu koma ga Allah da addu’a, Allah Ta’ala ne kawai zai kwace mu. Wannan al’amari mun shiga jidali ba kadan ba, saboda makiyanmu sun yi nazari sun yi shiri mummuna a kanmu kuma suna aiwatarwa. Kuma akwai wawaye wadanda su kuma a shirye suke su yi musu aiki in dai za a basu wani abu. Wannan kuma shine matsalar da muke fuskanta
Shi yasa in muka ce wannan shiri ne na makiya daga kasar waje, sai su ce to wane ne yake yi? Kai ka ga bature ne da idanunka ya zo yake yi? Kashe-kashen nan duk ku iku kuke kashe-kashenku. Wannan ya kashe wannan wannan ya kashe wannan, amma da hannun Bature a ciki.
Wa ya taba tambayar daga ina bindigogin nan suke fitowa? Wa ya taba tambayar wane ne ya basu tirenin? Ka san shirin wasu ne. Kowa ya san cewa wannan shiri ne da aka mana. To, iyaka abin da za mu iya cewa kenan, Allah dai ya kawo mana mafita.
ME YASA AKE LAKABAWA FULANI KOWANE BARNA?
Idan Bafullatani ya yi wani abu, to duk za ka ji kwayam; Fulani sun kai hari! Ko ma ba su bane, kawai sai a ce Fulani. Ka ga ‘yan fashi suna sa kayan Fulani, har su ma jami’an tsaro su kan sa kayan Fulani su yi ta’addanci ace Fulani ne. inda za ka gane, za ka ga takalmarsu, kuma ai Bafullatani ma yana da kamannu, amma su za ka ga gasu ga kamarsu suna “Pidgen”, irin yaren nan na ‘yan Kudu, amma sun saka irin wannan rigar, ‘yar sharer nan ta Fulani su yi ta’addanci, amma sai a ce Fulani.
Amma shi Bafullatani nasa ake fada, ba a fadin shi abin da aka yi masa. Yanzu ko ina sai su yi ta cewa Fulani sun yi kaza, Fulani sun kaza. To don me komai za ka ce Fulani ne mai yi? In ma fashi ne sai kace dan fashi ya yi fashi. Ba mu taba jin idan dan fashi sunansa Adebayo ne sai a ce Yarbawa sun yi fashi ba, ko in sunansa Okeke ne sai a ce Inyamurai sun yi fashi ba, ko in sunansa Tanko ne ace Hausawa sun yi fashi ba, ba haka ake cewa ba. To don me Bafullatani ya fita daban?
Shi Bafullatani shine kawai idan ya yi laifi sai a ce masa shi Bafullatani ne. In mutum ya yi laifi sai a ce ya yi laifi, amma ba a ce masa Bafullatani ya yi laifi ba. Dazu ake cewa a kan hanyar ko Birnin Kebbi ne, akwai inda su kan tsai da Bafullatani su harbe. Allah dai ya kiyaye.
JAWABIN SHAIKH ZAKZAKY (H) YAYIN ZIYARAR FULANI (5)
Za mu cigaba.
— Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Zakzaky (H).
Www.cibiyarwallafa.org
Tags
Jawaban Jagora