Na’am wannan wata sunna ce wadda ba ta canzawa. Matukar aka sami wasu mutane su na da wata manufa na kawo sauyi a cikin al’umma, to kai wa ga wannan buri yakan yi sakamakon wasunsu ya zama an kashe su, wasu sun ci wuya, wasu sun rasa dukiyoyi, wasu ma an kassara su, wasu an kore su daga kasa. Wannan ko da masu wata manufa ta siyasa ce, irin kamar a ce ’yan kwaminist, ko ma wane irin nau’i, ko wannan abin da aka ce ma dimokaradiyya a wadansu wurare wadanda suke cewa suna kira ga dimokradiyya. Za ka ga cewa akwai irin wadannan.
Kuma kan kira irin wadannan Shahidai, don shahada mutum yana iya yin ta a kowa ne irin tafarki, ko a kan menene ma, ana iya yin shahada. Wato shahada shi ne ba da rai a wani tafarki. Amma a gare mu shahada ana cewa fisabilillahi ne, shahada fi sabilillah, a tafarkin Allah, wato wajen tabbatar da addinin Allah. Wanda yake shi wannan shi ne a wurinmu shahada na sosai. Kodayake a luggace ana kiran mutane shahidai ko a kan ma menene, ko a wane sabil ne suka bayar da rayukansu. Kuma tarihi yakan gan su a matsayin gwaraza duk tsawon zamani.
Lokacin da na je wani gari a Mali, sunansa Janne. To sai muka je kusa da wani wuri sai aka nuna mani wani kabari aka ce wannan kabarin wata Shahidiya ce. To sai abin ya ba ni mamaki, Shahidiya kuma? Na ga irin ginin da ne. Sai aka ce eh wai tun zamanin da can su suna da wani irin nau’in canfi ko tsafi wanda suka dauka kogi yakan kawo kuma yakan share gari din.
Don garin kusan a da tsibiri ne kawai yake a tsakanin kogin Kwara na wancan lokacin. Don yanzu ma za ka sha mamaki, kogin ya janye ba shi ma kusa da wirin. Amma da can kamar tsibiri ne garin yake, kuma kogi ya rutsa da shi.
To duk shekara in kogin ya kawo yakan nemi ya share garin gaba daya, saboda haka a bisa irin nasu tunani a wancan lokacin , tun kafin bayyanar Musulunci, sai an ba kogin mutum. Saboda haka dodon kogin sai ya ce sai an ba shi ’yar Sarki, kuma shi Sarkin ya ce lalle ba zai bayar ba. Amma ita da ta ga cewa ta hanyar da za ta ceci mutanenta shi ne kawai ta sadaukar da ranta, sai ta zaga ta bayar da ranta. Saboda haka kabarinta ne ma suka sa. Ban san ko ya shekara nawa ba.
Domin wannan garin suna cewa ga dukkan alamu bincike ma wanda dan Adam ya yi yanzu, ya gano cewa wannan garin yana nan tun shekaka 3,000 da suka wuce. Kuma su ma mutanen garin suna tinkaho cewa wai cikin ‘Sahratu Fir’auna’ din nan, da aka ce “wa arsala fi mada’ini hashirina ya’atuka bi kulli sahharin alim.” An ce sun ce su ma daga cikin birninsu ma shi ma ya ba da mai sihiri wanda suka ce je su yi ’yar kure da Musa.
Ko haka ne ko ba haka bane, abin da ya sa na tuna da wannan maganar, wannan Shahidiya ce ta tsafi. Har nake cewa, to wannan menene na gaya mani, ni dauka Shahidiya ce fisabilillah. Amma su suna da kabarin nata su na girmamata.
A kasar Ingala ma nan akwai shigen wani abu mai kama da haka nan. Wanda aka ce ita ma wata ’yar Sarki ce, za a kawo masu hari sai bokaye suka ce in dai zai a da ’yarsa a yi tsafi da ita za a iya yin nasara. Sai Sarkin ya ce shi ba zai bayar ba. Aka ce ba da sanin sa ba sai ya zagaya ta ce ma bokayen, ga ta nan su yi tsafi da ita.
Wani bangaren na Jawabin Sayyid Zakzaky (h) a Taron Yaumusshuhada karona 18 wanda ya gudana a filin kofar Doka, Zariya.
Rubutawa Musa Muhammad Auwal
Copyright; Mu'assatusshuhada.
Tags
Jawaban Jagora