Saboda haka nan ma yakan zamana wani yakan gwammace ya yi gwarzontaka ya bar suna, ko da bai san da lahiran ba, bai ma yi imani da lahira ba, amma yana ganin cewa zai so ya yi gwarzontaka ya bar kyakkyawan suna. Har ma akwai karin maganar Bahaushe da ke cewa “a sayar da rai a nemo suna.” Wato wasu sukan ba da ransu don su samu suna.
Bature fakam da yawa yakan yi irin wannan, ya shiga wani KwaKwaf wanda yake yana so a ce shi ne wanda ya fara gano wuri kaza. Kamar akwai wani tsibiri wanda ake cewa ya fi kowanne bisa a duk duniya, shi ne tsibirin da aka sa wa suna ‘Everest,’ ina jin ko a Sirilanka yake? Can wajajen nan ne dai.
Akwai mutane da yawan gaske wadanda suka je suka bayar da ransu suka mutu wai a KoKarin a ce su suka hau tsororuwar tsauni din. Dutse ne mai tsini, yana da wahalar gaske a hau, amma Turawa da yawa sun je suna KoKarin a ce sune, kowa na KoKarin a ce shi ne ya iya hawa kan tsororuwar tsaunin. Har ma a jikin tsaunin an rubuta sunayen shahidan hawa tsaunin. Kuma haka nan bincike-bincike da yawan gaske wadanda wadansu sukan yi KoKarin su gano. Ko Mango Park da ya zo nan yana neman ya gano Karshen kogin Kwara, ai a kan ya gano kogin Kwara din, kafin ya gano ya yi shahada.
Haka nan za ka ga wasu suna KoKarin ko su binciko wani abu, ko su gano wani har su ma sai su sami shahada. Sai ya zama kuma an dauke su a matsayin gwaraza. Wato wannan ba ana tunanin za a sami lada ne a wajen Allah ba, ba a san da akwai Aljanna ba, ana tunanin kawai shi wannan ya sadaukar da ransa ne wajen gano wani abu. Ballantana a ce mutum ya sadaukar da ransa ne wajen gano abin da ya amfani mutane.
Kamar yadda aka ce akwai wani mutum wanda aka ce shi ya gano lantarki, wannan wanda muke amfani da shi. Har aka ce a KoKarin ya gano yadda wutar lantarkin ba za ta kama mutum ba, ‘Shocking’ din nan, to a haka shi ma lantarkin ya gama da shi. Yana KoKarin ya yi dabarar yadda ko ka tabi lantarkin ba zai yi maka komai ba. A haka nan ya cika, kuma shi yanzu gwarzo ne na gano lantarki. Duk lokacin da ake tarihin lantarki, za a kira sunansa.
Ba sai na ci gaba da ba da misalai ba, in ma na fadi wanna kalmar, cewa a bisa tarihin dan adam da al’adar dan adam, yana girmama wanda ya sadaukar da ransa saboda wani dalili. Ana ganin sa a matsayin Gwarzo ne. Idan dalili irin na siyasa ne yana iya zama gwarzon al’umma, wanda al’umma takan yi alfahari da shi. Ta ga cewa da gwazonsa ko ire-irensa suka samu suka cimma wata nasara.
Don haka ne ma in aka kawo wa Kasa hari, to wadanda suka ba da rayukansu wajen kare Kasar sukan zama gwarazan wadannan Kasashen. AKalla dai wannan shi ne a al’adance da a hankalce a ko’ina, ko da ya saba a Kasa kamar Nijeriya, wanda ba mu san ta ma san da wadanda suka murmutu wajen Kwato wa Nijeriya ’yancinta ko a yaKin basasan Nijeriya ba. Ba mu ma taba sanin wata rana ma da ake karrama su ba. Ko an yi sai dai na fatar baki.
Don ko bara da muka yi Yaumu Shuhada din nan, akwai wadanda suka rinKa fadin wannan maganar a gidan rediyo. Su abin da ya ba su mamaki shi ne mu muna da rana ta musamman ta karrama ranar shahidai, kuma har ana kula da ’ya’yan shahidai din, ana kula da rayuwarsu da kuma karatun yaran har ya zuwa iya yadda za su iya zuwa, amma sai suka kwatanta wannan. Wani gidan rediyo muka ji suna fadin wannan. Suna cewa abin mamaki a Kasar nan wadanda suka ba da rayukansu don ceto Kasar, su ba a yi masu wannan ba, ba wani wanda aka kula da ’ya’yansa. Bilhasali ma alal misali, mun san cewa wadanda aka tura suka je yaKin Laberiya, wadanda aka karkashe, ba a gaya wa matansu an karkashe su ba. Sai aka rinKa biyan su rabin albashin mazajensu ana ce masu suna nan. Wata rana kawai sai aka zo da sojoji aka kori matan da yaransu daga barikin soja, aka ce su bar wurin. Shi kenan, duk wacce mijinta ya mutu sai a kore ta kawai daga barikin soja, kawai shi kenan. Ta je ta san yadda za ta yi. Da ita da ’ya’yan ba bizines din wadanda suka tura su ne ba.
- Bangaren jawabin da Sayyid Ibraheem Zakzaky ya gabatar a wajen taron tunawa da Shahidan wannan Harka, ‘Yaumu Shuhada’ karo na 18 wanda ya gudana a filin kofar Doka, Zariya.
Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana daga kaset
Copyright-: Mu'assasatus-shuhada
Tags
Jawaban Jagora
