Offline

Jawabin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na Yaumil Mib’as 27 ga watan Rajab, 1435 (26/5/2014)

Jawabin Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na Yaumil Mib’as, wanda ya gudana da yammacin ranar Litinin din 27 ga watan Rajab, 1435 (26/5/2014). A muhallin Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya. Ammar Muhammad Rajab ya rubuta muku. Asha karatu Lafiyah. ‘Yan uwa Musulmi Assalamu alaikum warahmatullahi ta’ala wabarakatuhu. To, yau 27 ga watan Rajab hijira 1435. Kuma a rana mai kamar ta yau, 27 kenan da watan Rajab shekaran Giwa na da shekara 40, kafin hijirar Manzan allah da shekara 13 kenan. Ainihin aka aiko shi a matsayin Manzo ya zuwa dukkanin duniya. Dama can shi Manzo ne, tun kafin a haifeshi. Tun kafin yazo doron kasa shi dama Manzo ne. Shi ne, shugaban Manzanni. Bilhasali ma sauran Manzannni, Manzanninsa ne. Amma Allah ya kaddara shi ne zai zo a jeri a karshensu. Saboda haka tun ranar da aka dauki cikin Annabi, an dauki cikin Annabi ne. Yana ciki shi Annabi ne. Kuma kamar yadda duk Ma’asumai sukan Magana a ciki, ya kasamce yana Magana a cikin mahaifiyarsa. An haufeshi Manzo ne. Kuma kamar yadda duk Ma’asumai sukan Magana tun ranar da aka haife su, shima ya yi Magana lokacin da aka haifeshi. An ga ‘aja’ib’ da mu’ujozozi a samun cikinsa da haihuwarsa. Alal misali, wani abu da duk littattafai suka rubuta na tarihi, ‘khasatan wa Ama’, ya nuna cewa, ainihin ‘yan matan gari kowacce tana burin ya zama ta auri Abdullahi ne. Saboda da kyan da suke gani tare da shi. To, sai ya zamana Aminatu bnt Wahab (s.a) ita ce ta fifita a tsakaninsu, ita ce zabin Allah. Sai ya zama ita ce ta aure shi. Bayan da ta aure shi, bayan wani lokaci, sais u matan gari masu burin auranshi, sai suka ganin hasken da suke gani tare da shi. Har sukai mamaki, ah, wancan ko Abdullahi ne? Ina haskennan da muke gani? Ashe hasken ya yi ‘intikali’ zuwa Amina. Sai kuma aka ga yanzu Amina ita ce take da wannan hasken. To, sannan ta haifi wannan Manzo (s.a.w.w), sai hasken ya zama yana tare da shi. To, haka al’amarin yake. Saboda haka wani abu ne sananne. Ba ina baku labara ba ne. Ba Maulidi muke yi ba. Muna maganan Yaumul Mib’as ne. to, amma lokacin, Allah (T) ya ga daman shi wannan Manzo ba randa aka haife shi ne zai yi Magana ba. Saboda wata hikima irin ta Allah (T). Domin Isah dan Maryam (s.a) shi da mahaifiyarsa. Randa aka haifeshi, rannan ya yi Magana, ya ce; “Inni Abdullahi ata niyal kitaba wa yaja’ala ni Nabiyya.” Rannan, randa ta zo da shi jariri. Suna cewa; “ya aka yi ne kika zo da jariri alhali baki da miji?.” Tai ishara da su tambaye shi. Suka ce, ya za muyi Magana yaro a Gunya? Sai ya yi furuci, wanda da wannan furuci ya wanke mahaifiyarsa. Rannan ya fara Magana da Manzanci. Ka ga shi randa aka haife shi rannan ya fara isar da sako. Tun yana karamin Yaro. Kuma yana yaro ya kanje, gaddama ta sarke tsakaninshi da manya-manyan Malaman Masallaci. Su ce; wannan ba abin da Allah (T) ya fada a Attaura ba kenan, ku ne kuka jirkita. Abin da Allah (T) kaza ne. Saura su ce, ka ga yaro da ilimi dai. Ina ya yi karatu? To, ka ga shikenan wato.. Sannan kuma har wala yau dangane da annabi Yahaya. Allah (T) yana cewa; “wa atayna hul hukma sabiyya.” Masu fassara da yawa suna cewa; Muka ba shi Annabci yana yaro karami. Dangane da Dawud kuma, tun yana yaro karami shima kazalik. Shima aka ba shi Annabci yana yaro karami. To, amma me yasa shi wannan Manzon, shi ainihin tunda randa aka haifeshi bai fara wa’azi ba? Lokacin da yake yaro bai wa’azi ba? Amma dai suna ganin ‘aja’ib’ dangane da al’amuransa. Wannan saboda wata hikima wanda Allah (T) ya kimsa. Na Isah kana iya cewa; akwai hikiman da ya dace da wannan lokacin. Domin duk lokacin da aka aiko Annabi, kashe shi suke yi. Sai Allah ya turo musu Annabi wanda komai da komai na sa Mu’ujiza ce. Hatta ma haihuwarsa, sai ta zama ba yadda aka saba haihuwa aka haifeshi da shi. Sai ya zama wata tsarkakkan mace ta haifeshi ba tare da namiji ya tabe ta ba. Komai na Isah sai ya zama Mu’ujiza. Ta yadda ba yadda za a yi sui ya karyatawa. Amma duk da haka dai sun karyata din. Har suka yi aniyar kashe shi. Allah (T) ya tsamar da shi daga kaidinsu. To, shi kuma wannan wata hikima da Allah (T) haka yaso, na cewa, ainihin an dade a ‘kamfan’ Manzanni, tun bayan Annabi Ibrahimu da dansa Isma’ilu. Makkah ta dade ba tare da shiriya ba. Illa iyaka dan abin da ba a kan rasa ban a sunnan addinin Ibrahim wanda ya wanzu tare da su. Kamar sun kasamce suna wankan janaba. Kuma matansu na wankan karewar Haila da Nifasi. Kuma basu zai-ke-ma matansu a yayin Haila da Nifasi. Kuma basu cin mushe. Kuma suna da wa’insu ka’idodi wadanda suke irin dan ragowar abubuwa irin na shari’ar Ibrahim. Amma an dade da jirkita addinin Annabi Ibrahim. An maishe shi bautan Gumaka. Shima kansa Ibrahim din, an jirkita shi. An maishe shi wani abu daban. Ana tinkaho da jininsa ana wani addini daban. Addinin bautan gumaka ana kuma jingina masa. Harma a cikin Ka’aba, sunyi mutum-mutumi na wani dattijo suna nufin Ibrahim.

Post a Comment

Previous Post Next Post