Offline

BISA AL’ADAR DAN ADAM YANA GIRMAMA GWARZO

- Sayyid Zakzaky (h)
Don haka shi ma aka ce akwai inda suka yi mutum-mutuminta, suna zuwa su rinka watsa su manja da goro da sauransu. Duk da cewa tun a jahiliyya su suke da wannan labarin.

Ina kawo maku wadananan ’yan misalan ne in nuna cewa bisa al’adar dan Adam yana girmama gwarzo wanda ya ba da ransa a tafarki, kowane irin tafarki ne. La’alla ko don kare gari ne ko don ceton rai ne ko domin kawo wa mutane wani irin abin da zai amfane sune, ko don ya tunkude masu wani irin nau’in cuta. In har ya sadaukar da ransa a wannan, to yakan zama gwarzo a wajensu, tsawon tarihi.

Don haka in ka duba tarihi za ka ga tarihin gwaraza. Har ma nau’o’in gwarzontaka a wajen wadansu har da mutum ya kashe kansa. In alal misali a yi masa raini ne ya ga cewa shi da ya dauki raini din gara ma ya mutu, sai ya kashe kansa, har ma sai a sara ma gawar a ce shi gwarzo ne. Kuma har yanzu. Ko a cikin wadansu kabilolin da muke tare da su din nan akwai masu wani abu mai kama da haka nan.

Alal misali, kodayake ba ni da lokaci mai tsawo da zan iya kawo maku daban-daban na yadda mutane sukan girmama gwarzo ko a wace irin akida suke da shi, kowane irin addini suke da shi kowane irin tunani suke da shi, bisa al’adar dan Adam yana girmama gwarzo.

Akwai wasu, wannan ban san ko dariya zai ba mutane ba, ko mamaki, ko haushi. Akwai wadansu kabila a cikin Igbo wadanda suke zaune a wani da ake ce ma Anambra, Anambra din gari ne ba jihar Anambura ba, ban san ma ko garin yana cikin jihar Anambra ta yanzu bane ko yana cikin Enugu, amma dai sunan garin kenan, Anambra. Wadanda aka ce su ba sa karbar raini, kan abu dan kadan su sai su kashe kansu, kuma su a wurinsu abin gwarzontaka ne.

Wani yana ba ni labari ya ce ai su suna jin tsoron ’yan Anambra, saboda ko rigima kuka yi da shi, shi ba zai dauki raini ba, sai ya kashe ka ya kashe kansa. Aka ce ma akwai ma wani wanda aka je biki, walima. Shi kenan mai bikin ya mike ya ce don Allah a yi hakuri ba isasshen tabar da za a ba kowa kara daya. Saboda haka mutum biyu za a ba su kara daya ne su raba na taba, a wajen biki din. To sai a ce kai da kai kara daya. Sai su gutsira, sai wannan ya busa wannan ya busa kowa ya sha.

To sai aka je wajen wasu aka ce da kai da wannan, sai aka ba su kara daya. Shi wannan sai ya dubi wannan ya yi masa kallon raini, ya gan shi wajila-wajila. Ya ce “gaskiya ni ba zan raba taba da wannan ba.” Sai ya dauko tabar ya cinna mata wuta ya dinga busa bin sa yana kallonsa har yana busa masa hayaki.

Haka nan dai aka gama, kowa ya sha rabin sugari, amma shi wannan mutumin bai sha rabin ba domin abokin rabonsa ya shanye masa ragowar rabin. Saboda haka sai ya koma gida ya gaya wa babansa cewa a wajen biki ga abin da ka yi m asa. Ya ce kai da na ne kuwa? Mutumin da ya hanaka taba din yana nan da rai? Ya ce yana na da rai. Ya ce shi ne ka zo kake gaya mani? Kai ni na haife ka kuwa da za a yi maka wannan wulakancin ka dauka?
To aka ce wannan sai ya tashi kawai ya je ya sami wancan, shi kuma ya dawo gidan biki yana tafiyar tinkaho, sai shi da ya sha karan sigari daya a inda kowa ya sha rabi. Sannan ya same shi ya banke shi ya caka masa wuka ya kashe. Sannan ya dawo ya gaya wa Babansa, ya ce Baba na kashe shi. Sai ya ba shi hannu suka gaisa ya ce “ka tabbata da, mu ba mu daukar raini.” Saboda haka sai ya dauko igiya ya ba shi, yanzu zai rataye kansa. Sai ya je ya rataye kansa.

An ce a kabilarsu, in mutum ya rataye kansa, akan zo da ganga ne a inda ya rataye kansa din a buga a yi rawa, gwarzo ne shi. Wannan kan bai dauki raini akan an hana shi karan sigari, ba zai dauki rainin wannan ba, ya gwammace ya mutu .

Wannan ba ina ba ku misali akan cewa wadannan abubuwan kirki ne da ya kamata a kwafa ba. Ina ba da misali ne akan cewa bisa al’adar mutane ko su waye suna girmama gwarzo.

-- Bangaren jawabin da Sayyid Ibraheem Zakzaky ya gabatar a wajen taron tunawa da Shahidan wannan Harka, ‘Yaumu Shuhada’ karo na 18 wanda ya gudana a filin kofar Doka, Zariya. 
Musa Muhammad Awwal ne ya rubuto mana daga kaset

Copyright-: Mu'assasatus-shuhada

Post a Comment

Previous Post Next Post