Imam Muhammad Al-Jawad(as), d’an Imam Ali Ar-Rida(as), d’an Imam Musa Al-Kazim(as), d’an Imam Ja’afar As-Sadiq(as), d’an Imam Muhammad Al-bakir(as), d’an Ali Zainul-Abidin(as), d’an Imam Husain Sayyidus-Shuhada(as); kanin Imam Hasan Al-Mujtaba(as), ‘ya’ya Ali bin Abi Talib(as) da Fatimah Az-Zahra(as); ‘yar Annabi Muhammad(saw).
Al-kunyayarsa: Abu Jaffer al-Thani…
Lakabinsa: At-Taqi, Al-Jawad…
Mahaifiyarsa: Hazrat Bibi Sabika Khatoon, (Khaizuran).
Ranar da aka haifeshi: 10 ga watan Rajab, 195 Hijiriyya. April 12, 811 CE, (809 AD)
Gurin haihuwarsa: Madina.
Farkon imamancinsa: 29 Safar 203/ 9 September 818. (819 – 835 CE).
Wanda ya gajeshi: Ali b. Muhammad al-Hadi(as).
Wanda ya gada: Ali al-Ridha(as).
Tsawon shekarun imamancinsa: 17 years.
Shekarunsa: 25.
Matansa: Samana, Umm al-Fadl.
Yayansa: Ali, Musa, Fatima, Amama.
Lokacin Shahadarsa: 29 ga watan Zul-Qaad 220 H. 29 November 835 CE.
A wata ruwaya; 6 ga watan Dhu al-Hijjah, 220 H.
Gurin da yayi Shahada: Kazmain.
Dalilin Shahadarsa: Gubar da Khalifan Abbasiyawa Mu’atasim yasa aka saka masa.
Gurin da kabarinsa yake: Kazmain, kusa da Baghdad (IRAQ).
Imam Muhammad Jawad(as) shine Jagoran shiriya na 9 cikin jerin jagororin 12 da Annabi Muhammad(saw) ya yi bushara da samuwansu a bayansa, kuma ya bayyana kasantuwarsu da daukakan addinin musulunci, sannan ya rubanya su da Al-kur’ani mai tsarki saboda tsarkakansu, kuma ya yi wasici da yin riko da su gaba daya, kuma ya siffantasu da jirgin tsira; wanda ya hau ya tsira wanda kuma ya saba ya halaka, kofar tuba wanda ya shiga an gafarta masa, hujjojin Allah a bayan kasa, magada ilimin Annabawa da Manzonni, mabubbugar hikima….
An haifi Imam Muhammad Jawad(as) ne a daren jumma’a 10 ga watan Rajab, shekara 195 bayan hijira, a birnin Madinah.
Mahaifiyarsa ita ce Subaikatu wadda ta hada zuriya da Mariyatul-Kibdiyya matar Manzon Allah(saw), wadda ita ce mahaifiyar dansa Ibrahim, kuma ana kiranta da Raihanatu ko Durratu, wanda mijinta Imam Ali Arridha(as) ya ke kiranta da Khaizaran.
Har ila yau: Imam Hasan Al-Askari(as) yana bayyana Subaikatu da cewa an halicceta tsarkakekkiya wadda aka tsarkake. Ana kinawa wa Subaikatu da Ummul-Jawad ko Ummul-Hasan wadda ta kasance mafi daukakan matan zamaninta.
Farin ciki da murna sun lullube Imam Ali Ar-ridha(as) sakamakon haifa masa da mai albarka da Subaikatu ta yi, wanda yake cewa hakika an haifa mini da da ke kama da Musa dan Imrana da ya raba teku gida biyu, kuma mai kama da Isa dan Maryam, Uwar da ta haifeshi ta tsarkaka.
Kyawawan Dabi’un Jagoran Shiriya na 9; Imam Muhammad Jawad(as):
Kasancewar babu makawa mutumin da shi ne jagoran shiriya da Allah Madaukakin Sarki ya daurawa alhaki shiryar da al’ummah zuwa ga hanya madaidaiciya, tare da bambance tsakanin gaskiya da bata, ya zame shi ne mafi sanin mutane a zamaninsa kuma wanda yafi kowa fahimtar al’amuran shari’a da hukunce hukuncen addini, tare da sanin harkokin siyasa da gudanar da al’amuran mutane kuma mafi daukakan mutane a fagen kyawawan dabi’u da cikan kamala. Hakika Imam Muhammad Jawad(as) duk da kasancewarsa mai karancin shekaru a duniya lokacin da ya karbi ragamar jagorancin al’ummah a bayan mahaifinsa, amma ya zame tauraro a fagen ilimi, cikan hankali da kaifin basira wanda ya kera duk wani mai matsayi ko daukaki a zamaninsa.
Malaman fiqihu da masana a fagen fannonin ilimi daban daban da suka jarabashi ta hanyar gudanar da mahawarori da gabatar da tambayoyi masu tsauri gare shi sun samu gamsassun amsoshi da suke yaye shamaki da kawar da duk wani kokwanto da rudu a cikin zukata. Sakamakon haka masana da manazarta suka mika kai ga tabbas da hakika, suka rungume shi a matsayin jagoran shiriya wanda haka ya sanya tafarkin Iyalan gidan manzon Allah(saw) ya kara habaka da watsuwa a tsakanin mutane.
A fagen kyawawan dabi’u kuwa, Imam Muhammad Jawad(as) ya ci gaba da wanzar da dabi’un magabatansa ne da dukkanin rayuwarsu ta zame darasi ga al’ummah, domin sune wadanda suka gaji kyawawan dabi’un kakansu da Allah Madaukakin Sarki ya bayyana shi da cewa:
“Kuma hakika kana kan kyawawan dabi’u masu girma”.
Hakika Imam Muhammad Jawad(as) ya kasance wanda yafi al’umman zamaninsa yawan bautan Allah da biyayya gare shi, matsayinsa a fagen kyawawan dabi’u daidai yake da magabatansa shugabannin shiriya na Iyalan gidan manzon Allah(saw) wadanda suka sadaukar da dukkanin rayuwarsu wajen aikata dukkanin abin da zai kusantar da su ga Allah madaukaki.
Malaman tarihi da mutanen da suka rayu tare da Imam Muhammad Jawad(as) sun bayyana shi da cewa mai yawan salloli ne da tsawaita munajati da mahaliccinsa.
Yazo cikin littafin Mustadrak Awa’limul-Ulum cewa; Imam Muhammad Jawad(as) ya kasance idan sabon wata ya kama ya kan yi sallah ta nafila raka’a biyu, a raka’ar farko yana karanta fatiha da suratul-Ikhlas sau talatin daidai da ranakun wata, sannan a raka’a ta biyu ya karanta fatihah da suratul-Qadir sau talatin, bayan nan ya yi sadaka da abin da ya sauwaka gare shi domin neman amincin watan a wajen Allah madaukakin sarki, kuma kasance yana raya dare da salloli da karatun Al-kur’ani gami da karanta addu’o’i, don haka mutanen da suke tare da shi suka ruwaito tarin addu’o’i da munajatin da yake karantawa.
Haka nan Imam Muhammad Jawad(as) ya kasance mai yawan gudanar da aiki hajji a lokacin rayuwarsa. Imam Muhammad Jawad(as) ya kasance mai yawan kyauta da taimakon mutane wanda saboda tsananin kyautansa da karamcinsa ne mutane suke masa lakabi da Jawad wato mai yawan kyauta da karamci.
Maganganun Yabo Da Aka Yi Kan Imam Muhammad Jawad(as):
Hakika girman matsayi da daukakan da Allah ya huwace wa Imam Muhammad Jawad(saw) sun shige tunanin mutanen da suka yi zamani da shi, saboda haka suka tasirantu da shi zukatansu suka kaunace shi, kuma babu wani da zai zauna ko ya tattauna da shi har sai ya rusuna masa tare da yin furuci da daukakan matsayinsa da shaida kan cancantarsa ga matsayin jagorancin al’ummah zuwa ga hanya madaidaiciya, sakamakon zurfin iliminsa, kaifin basira da zurfin tunaninsa, cikan hankalinsa da kyawawan dabi’unsa.
Don haka malaman musulunci suka yi maganganun yabo tare da rubuce rubuce kan girman matsayinsa da daukakansa kamar yadda suka yi kan magabatansa shugabannin shiriya na Iyalan gidan manzon Allah(saw) wanda zamu ambaci wasu daga cikin maganganun kamar haka:
Sibdu bin Jauzi Al-hanafi a cikin littafinsa na Tazkiratul-Khawas yana cewa; shi ne Muhammad dan Ali dan Musa dan Ja’afar dan Muhammad dan Ali dan Husain dan Ali dan Abi-Talib(as). Ana masa kinaya da Abu-Ja’afar, kuma ya kasance a kan tafarkin mahaifinsa a fagen ilimi, tsoron Allah, gudun duniya da taimakon mutane.
Az-Zahabi a cikin littafin Tarikhul-Islam yana cewa; Muhammad ya kasance ana masa lakabi da Jawad, Alqani’u da Almurtadha kuma ya kasance daga cikin shugabannin Iyalan gidan manzon Allah(saw) sannan ya kasance daya daga cikin wadanda ake siffantasu da yawan kyauta da taimako, don haka ake masa lakabi da Jawad wato mai yawan karamci da kyauta.
Ibnu Sabbaghil-Maliki a cikin littafinsa na fusulul-Muhimma yana cewa; Muhammad Jawad shi ne jagoran shiriya na tara, an fi saninsa da Abu-Ja’afar Assani, kuma duk da kasancewarsa mai karancin shekaru a duniya amma ya kasance mai girman matsayi da daukakan ambato, kuma ya zame jagoran shiriya ne a bayan shahadar mahaifinsa Imam Ali dan Musa Arridha bisa nassin da aka yi masa da kuma isharan da mahaifinsa ya yi a kansa na kasancewa wanda zai gajeshi a bayansa.
Shahadar Imam Muhammad Jawad(as). Hakika khalifan daular Abasiyawa Muhammad dan Haruna Rashid da aka fi sani da Mu’atasim ya ji tsoron kasancewar Imam Muhammad Jawad(as) nesa da shi, don haka ya dauki matakin tilasta masa dawowa kusa da shi ta hanyar bada umurni wa jami’an tsaro kan su tafi birnin Madinah su taho masa da Imam Jawad(as) zuwa Bagadaza saboda ya samu daman sanya ido kan dukkanin harkokinsa(as) inda jami’an tsaron suka tafi suka taho da Imam Muhammad Jawad(as) zuwa birnin Bagadaza a karshen watan muharram na shekara ta dari biyu da ashirin bayan hijira, kuma ya yi shahada ne a watan zul-qa’adah na wannan shekarar.
Hakika Imam Muhammad Jawad(as) ya zame wani babban barazana ga mahukuntan daular Abasiyawa sakamakon kasancewarsa Jagoran shiriya daga iyalan gidan Manzon Allah(saw) sannan rawar da yake takawa wajen wayar da kan al’umma da ilimantar da mutane fannonin ilimummuka musamman ma ilimin addinin musulunci suna daga hankulan mahukunta daular Abasiyawa da suke bukatar ganin al’umma tana rayuwa cikin duhun jahilci domin su samu damar ci gaba da gudanar da bakin mulkinsu na kama karya, kuma mahukuntan suna zargin Imam Jawad(as) da hannu a boren da al’umma keyi wa mahukunta sakamakon bakar siyasar zalunci da kama karya da ake gallaza musu, don haka mahukuntan daular ta Abasiyawa suka dauki matakin aikewa da shi lahira.
Ibnu Asir a cikin littafin tarihinsa na Kamil yana cewa:- Khalifan daular Abasiyawa Mu’atasim ya kasance mai karancin tunani da karkata zuwa ga kekashewar zuciya wajen ma’amala da abokan adawarsa ta fuskar siyasa, kuma ya kasance ba shi da kwarewa ta siyasa da haka zai bashi damar gudanar da harkokin mulki, don haka a lokacin mulkinsa ya fuskanci yawan boren siyasa a sassa daban daban da suke karkashin daular Abasiyawa. Don haka yayin da khalifan daular Abasiyawa Ma’atasim ya aike a zo masa da Imam Muhammad Jawad(as) daga Madinah Isma’il dan Mihran ya zo yake cewa Imam Muhammad Jawad(as): “Ya shugabana ga shi zaka fice daga Madinah, shin wannan al’amari na Jagoranci wajen wa zai koma a bayanka? Sai Imam Muhammad Jawad(as) ya dube shi idanunsa suna fitar da hawaye, wanda har hawayen ya jika masa gemu, sannan yake cewa Isma’il dan Mihran a wannan lokaci ne za’a ji mini tsoron mutuwa, don haka matsayin Jagorancin shiriya a bayana yana ga dana ne Ali”.
Khalifah Mu’atasim ya yi ta tunanin hanyar da zai bi ya aiwatar da kisan gilla kan Imam Muhammad Jawad(as) ba tare da mutane sun zarge shi da hannu a kisar ba, wanda daga karshe ya bi ta hannun matar Imam Jawad(as) wato Ummul-Fadhil yar khalifa Ma’amun wato yar dan uwansa. Khalifah Mu’atasim ya zabi Ummul-Fadhil a matsayin wadda zata aiwatar da kisan gilla kan Imam Jawad(as) ne domin zai yi wuya mutane su fahimci cewa mahukunta suna da hannu a kashe shi, kuma Ummul-Fadhil ta amince ta dauki alhakin aikata wannan mummunan laifi na aiwatar da kisan gilla kan jikan Manzon Allah(saw) kuma Jagoran shiriya ne bisa wasu dalilai kamar haka:
1. Ummul-Fadhil ta kasance jinin sarauta ce da take jin kanta, domin diya ce ga khalifan daular Abasiyawa Ma’amun kuma baffanta Mu’atasim ne ya karbi ragamar mulki a bayan mahaifinta, kuma imani bai ratsa Ummul-Fadhil ba ballantana ta fifita jinin Manzon Allah(saw) a kan dangantakarta, saboda haka ta tasirantu da zigon baffanta ta fifita duniya a kan lahira, ta amince ta kashe mijinta domin mulkin kama karyan gidansu ya ci gaba da wanzuwa a bayan kasa.
2. Ummul-Fadhil ta kasance tana fushi tare da kiyayya da mijinta Imam Muhammad Jawad(saw) saboda ya kara aure da ya yi wato ya yi mata kishiyoyi, kuma babban karin tashin hankali a gare ta bata haihu da shi ba, sai ga kishiyarta da ta zo a bayanta ta haifa wa Imam Jawad(as) yaro na miji da ya sanya masa suna Aliyu Hadi(as). Hakika mummunan kishin da Ummul-Fadhil ke yi ya watsu a tsakanin mutane, wanda har malaman tarihi suka nakalto a cikin littattafansu, misali kan haka:
Ya zo cikin littafin Kashful-Ghummah cewa: Ummul-Fadhil ta rubuta wasika zuwa ga mahaifinta khalifah Ma’amun tana koka masa cewa mijinta yana bata mata rai saboda auren da ya kara, sai mahaifinta Ma’amun ya rubuta mata martani da cewa bai aurar da ita ga Imam Jawad(as) domin ya haramta masa abin da yake halal ne gare shi ba, kuma kada ta sake kawo masa irin wannan karar.
Khalifan daular Abasiyawa Mu’atasim ya yi amfani da kishin da Ummul-Fadhil ta wurga kanta ciki wajen ingizata cikin masifa da nadama ta har abada wanda ya aiko mata da ruwan inabi mai guba kan ta shayar da mijinta Imam Muhammad Jawad(as). Shaidan ya riga ya hure wa Ummul-Fadhil kunne don haka ta amsa kiransa ta kawo ruwan inabin da baffanta ya aiko mata da shi ta sanyawa Imam Muhammad Jawad(saw) a gaba, bayan Imam Jawad ya sha, sai Ummul-Fadhil ta nuna damuwanta har da kuka, sai Imam Muhammad Jawad(as) ke ce mata mene ne na kuka? bayan kin aiwatar da makircin da aka umurceki da aikatawa, iyaka dai wallahi Allah zai jarabeki da tsananin talauci da masifa a rayuwarki. Hakika Allah ya jarabi Ummul-Fadhil da cuta mai tsanani da ya kai ga ta batar da dukkanin abin da ta mallaka wajen neman magani, har ta kai ga tana neman taimako, kuma daga karshe tayi mutuwan wulakanci a wani waje ita kadai wadda sai daga baya aka gano cewa ta halaka.
Gubar da aka shayar da Imam Muhammad Jawad(as) ta yi tasiri a jikinsa har ya kai ga karshen nunfashinsa yana ambaton Allah Madaukakin Sarki.
Hakika khalifan daular Abasiyawa Mu’atasim ya kawar da hasken musulunci da ya haskaka tunanin mutane da zuciyarsu wanda ya yi sanadiyyar fitar da al’umma daga duhun jahilci da bata.
Bayan an shirya tsarkakekkiyar gawar Imam Muhammad Jawad(as) khalifan daular Abasiyawa Mu’atasim da dansa Wasiq suna daga cikin mutanen da suke sahun gaba wajen yi wa Imam Jawad(as) sallah domin wanke kansu daga zargin hannu a kisarsa, wanda mutanen Bagadaza suka fito kwansu da kwarkwatarsu suna nuna bakin ciki da alhininsu dangane da shahadar Imam Jawad(as) wanda aka bisineshi a makabartan Kuraishawa da ke birnin Bagadaza kusa da kabarin kakansa Imam Musa Al-Kazim(as).
Imam Muhammad Jawad(as) ya yi shahada ne sakamakon shayar da shi guba da aka yi yana da shekaru ashirin da biyar a duniya, don haka shi ne jagoran shiriya da yafi karancin shekaru a tsakanin Jagororin shiriya goma sha biyu da Manzon Allah(saw) ya yi bushara da samuwarsu a bayansa, wanda ya gudanar da dukkanin rayuwarsa wajen yada hakikanin koyarwar addinin musulunci. Imam Muhammad Jawad(as) ya yi shahada ne a karshen watan Zul-qa’ada ko Zul-Hajj, shekara ta dari biyu da ashirin bayan hijira.
Amincin Allah ya tabbata a gare shi ranar da aka haife shi, da ranar da ya yi shahada yana kan hanyar Ubangijinsa!
Abdulrahman Murtala
abdulrahmanyj@gmail.com
Tags
Munasaba