.
A ranar Talata 10 ga watan Fabarairu, 2015, Mabiya Malam Zakzaky suke ta aiki a cikin muhallinsu Husainiyyah Bakiyyatullah, Zariya, an kammala wannan aiki da aka dauri aniyar yi a wadannan kwanaki. Sai dai kuma daga zuwa lokacin kadan sun ci gaba.
Masu aikin sun hada matasa masu karfi a jika, da yara kanana. Da kuma Manyan mutane. Duk wanda ka tambaya, zaka ji shi ya kawo kan shi wajen wannan aiki domin yin tarayya wajen gina wannan muhalli.
Sai dai a tun daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Disambar shekarar 2015 biyo bayan wani mummunan hari da Sojojin Najeriya suka yi a wajen inda aka kashe mutane da daman gaske, daga ƙarshe an rushe gurin gaba ɗaya ya zama Kango.
Tags
Zaria Massacre