—Jamilu Musa Usman
Ni a Bauchi nake kuma daya daga cikin jagororin a Mu'assatu Abul Fadl. Da farko dai muna cikin gida a Gyallesu, gidan Malam Zakzaky, muna shirye-shiryen maulidi, domin a ranar za mu sanya tutar ranar daya ga watan Maulidi, kawai sai muka samu sakon waya cewar Husainiyya fa an rufe su. Nan take muka kamo hanya zuwa Husainiyya. Muna isowa, tun daga wajajen PZ, sai muka fara ganin sojoji daddaya-daddaya, an yi layin da su. Haka dai sai muka karasa Husainiyya. Isar mu, sai muka samu har an farfasa duwatsu a kan titunan, sai muka tambayi yan'uwa cewa, me ya faru? Sai suka ce mana lallai sojoji ne suka zo haka siddan nan gaban Husainiyya wajen gidan man nan, har ma sun yi harbi. Sai muka ce wa yan uwa lallai in dai sun yi harbi, to tabbas waki'a ce. Sun zo kisa ne. Har jikin Husainiyya me ya kawo soja? Nan take sai aka ce mana ai har ma sun riga sun yi kisan ma. Na gangara kasa, can inda sojojin suke tare da 'yan uwa. Lokacin yan'uwa suna ce wa sojojin su tafi, su tafi, Su bar musu wajen domin ba su da aminci da su.
Muna wajen, sai ga tawagar Burutai ta iso wajen. A lokacin da ya iso wajen, sai Burazu suka ce lallai babu wani wucewar da wani zai yi, domin babu aminci a tare da ku. Yanzu muna kokarin ma'aikatanku da suke gaban Husainiyya su tashi, yanzu kuma kun zo kuna ce mana zaku sake wucewa. Haka dai 'yan'uwa suka ki aminta da wucewar. A lokacin, da sojojin suka yi magana, sai 'yan'uwa suka ce musu yanzun nan kuka wuce, kuka kashe mana mutane babu gaira babu dalili. A wannan lokacin ne Sani Usman Kuka Sheka ya fito tare da masu daukan bidiyo ya yi ta rantsuwa, yana cewa a ba su hanya, su wucewa za su yi. Burazu dai suka sake maimaita cewa lallai ba za su wuce ba, domin yanzu kuka kashe mana mutane basu yi maku komai ba. Akan wane dalilin za mu sake aminta da ku?
Kashe kyamaransu da suka yi ke da wuya, sai suka bayar da umurni, aka ci gaba da kashe burazu, babu yaro, ba babba, ba mace, ba namiji, duk kashewa sojojin suke yi. Zan iya tunawa, ni wacce sojojin suka fara kashewa a
gabana, wata yarinya ce, ba ta wuce shekara takwas ba. Suka kashe ta nan take. A kai suka same ta. Sai kuma wani Buraza mai hannu daya, wanda suka harba a wakiar Kudus. A wannan waki'ar kuma suka karasa shi yana takbir, yana Allahu akbar, suka kashe shi, mai suna Sufi. Haka nan suka ci gaba da kashe Burazu, kawai kai ka ce sun fito yaki a tsakanin kasa da kasa ne.
Gaskiya, a lokacin da yake sun nunnunka 'yan'uwa a yawa, domin sun karo karfi fiye da yadda ba ka tsammani, ala tilas suka sa 'yan'uwa suka koma cikin Husainiyya. Da muka koma, mun dauka shi ke nan, tunda sun ce hanya suke so. Ga shi sun kashe mu, kuma mun bar musu kan titin. sai su yi me inda gaske ne? Sai su wuce, amma ina! ai zan iya ce maka lokacin ne aka fara.
Abin mamaki, sai ga sojojin kasar nan sun zagaye ko ta ina Husainiyya. Babu wata hanyar da ba su yi mata kofar rago ba. Zagayewansu ke da wuya, akwai wani daki a saman Husainiyya, sai mu muka shiga. Muka ga yau ne, gobe ne, sai fa muka ga karo yawan sojojin kawai ake yi.
Can dai muna wannan yanayin, sai muka ji wucewar Gwamnan jihar Kaduna, El-Rufa'i. Har muna tsamnanin cewa tun da yanzu ya zo, ya kuma gane wa idonsa irin kisan da ake mana a lokacin, kuma tun da shi ne Chief Security officer na jihar Kaduna, to zai yi masu magana. Muna zaune dai sojoji sun zagaye mu, ba su kuma tashi ba; mu kuma dai muna ciki muna ta kabbarori. Ana haka, can sai muka ga wata katuwar mota ta dauko wani kwantena. Buďe shi ke da wuya, sai muka ga makamai ne iya ganinka.
Daga cikin abubuwan da ni na iya tantancewa a cikin wannan kwantenar na ga kwalin harsasai, debo su kawai ake yi ana jibgewa a kusa da Husainiyya. Haka nan sun kawo wasu muggan makaman da ban iya gane da me, da me
ba ne. Haka dai muna zaune tun karfe uku na yamma ba su yi harbi ba; wajajen karfe goma da kwata, kwatsam me za muji? Sai suka harbo mana RPG (Rapid propelled gurnet), ya bugi gefen Husainiyya sai da ya rusa rabin ginin. Shi ke nan dai muna wannan yanayin, sai suka yi layi. Su zo su saki wuta, su saki wuta kawai, su kuma 'yan'uwa suna kwakkwance a kasa suna kabbarori.
Idan suka yi kamar mintina talatin suna harbi, sai su koma, sai a canza wasu. A wajen canjin sukan dauki kamar goma. A dan wannan minti goman ne kadai muke samu mu sarara. Can sai ka sake jin sun sake harbo RPG. Sai su sako tanka a gaba, sojoji na bin bayanta. Muddin ta harbe ka, duk inda ta same ka, sai ya rabe. In kafa ne, ko hannu, lallai sai ta raba. In kuma ta same ka a ciki, ko kai lallai ba rauni zai zama ba; dole ne sai ka tafi kawai,
domin harbin ta ya wuce misali. Abin da ya faru shi ne harbin suna yi mana kusa-kusa ne, don haka harbin yakan shige mu ne da karfinsa.
Ba su bar mu haka ba; sun yi ta harbo RPG, ga tankokin yaki, ga sojoji suna bin su a gafe, hagun da dama. Idan suka zo, wuta kawai suke yi kan ko ma waye. Bayan sun yi luguden wuta, in sun gaji sai su koma. A jin kunnena, na ji sojojin sun harbo mana RPG sama da biyar, a iyaka wanda na ji da kunnena. A lokacin da suke harba RPG a cikin dare, mun dauka muddin gari ya waye za su ji kunyan idon jama'a wajen harba mana irin waďannan muggan makaman. Ai kuwa me Zai faru? Wajajen karfe biyar na asuba, sai suka zo suka zo mana ta baki biyu, kofar gaban Husainiyya, tun cikin dare suke son shigowa ta wajen, amma 'yan'uwa suka jajirce, suka hana su damar shiga. Duk da suna kisan kiyashi, amma dai sun gagara shiga. Sai kuma kofar tsakiya, wanda shi bai da wani karfi. Da asuban kawai muka ga sun danno da tankoki ta wađanan kofofin. Danno kai cikin tsakiyar da tankokinsu suka yi, a wannan lokacin ne sojojin kasar nan suka yi kisan da zan iya ce maka ya wuce na kiyashi, domin kisa ne suka yi, babu yaro, babu babba. Ba wai wannan mace ce, a'a wannan namiji ne ba. Kisan kawai suke yi. Sun yi mana kisan muhaukaciyar kisa iyaka son ransu.
BA SU IYA KAMA DAN UWA KO DAYA BA SAI DA
SUKA YAUDARE MU
Akwai wasu 'yan'uwa da suka dan buya a wasu wurare, sai sojojin suka zo suna sanarwar cewa, duk wanda yake wani waje ya yi saranda, ba za su kashe shi ba. Suka ce, duk wanda ya fito kafin su kirga goma, sun dauki alkawarin ba za su kashe shi ba. Haka zalika sojojin sun ce wa 'yan'uwa duk wanda ya fito, ko da ciwo a jikinsa za su kai shi asibiti; in mutum ba shi da rauni kuma ya daga hannunsa ya dora a kan wuyansa, to ba za su taba mutum ba. Bari na takaita maka, wallahi bayan sun yi alkawari, duk wanda ya fito a
wannan fitowar na farko, sai suka tara 'yan'uwa waje guda suka rinka dambara musu harsasai a kafa. Suka yi musu daurin da me zan misalta maka ne ma? Sannan sun yi ta amfani da hijaban jikin sistoci suna daure burazu da shi. In kika fito, sai su yanka hijab dinki, su daure namiji da shi. Haka suka yi ta yi.
Muna wannan yanayin, bayan sun tafi da wadanda suka kama, sun hada su da wadanda suka jikkata, sai kuma suka zo suka bunka wa gawawwakin da suka kashe wuta. A lokacin da suka ce a yi saranda, gaskiya ni ban yarda na yi ba; ko ba komai na fara ganin suna ta harbin wadanda suka rika yin sarandan. Ka ga yaudara ke nan. Ina cikin wani daki a cikin Husainiyya, dakin kusa da dakin sauti, inda aka ajiye majinyata da kuma gawawwakin 'yan'uwa, ciki har da na Gabari din nan, da kuma shahidan wannan ranar.
Muna tare da wani Haris da wata Sista. Ita Sistan ta ce lallai za ta fita. Har ma ta cire kalimatul bara'a da ke kaina ta daura min a inda aka harbe ni, sakamakon jini yana ta zuba. Sai ta bi cikin wadanda suka yi saranda, aka kuma kama su. Sai nake ce wa shi daya Haris din ko da za muyi shahada, lallai kar mu yarda mu yi saranda; ni dai shawara ke nan. Da na yi saranda, gara sun kashe ni a nan. Muna wannan yanayin, shi Haris din ya ji shawarata. Muna zaune a cikin gawawwaki da majinyata, can sai suka zo suka bankado kofar dakin. Muna kallon su suka sake sakin wuta a cikin wajen. Da yake ginin Husainiyya yana da kariya daga harbi saboda yanayin ginin, sai ya zama ba su iya samun mu a wannan lokacin ba. Sai muka ki fitowa. Saina ji suna ta sanarwar in da sauran mutane su fito. Shigowarsu ke da wuya, sai shi Haris din ya yi wani motsi ta bayan kofa
Sai suka ji motsinsa suka saki wuta a wajen, nan take ya yi shahada, domin in sun ji motsi, ba wai sukan yi harbi biyu,
uku ba ne, a'a sakin wuta kawai suke yi. Mutum daya za su iya yi masa harbi ashirin, ta yadda ko ta yaya ne, sai mutum
ya yi shahada.
Bayan wannan Haris din ya yi shahada a gabana, sannan akwai wani wanda aka harbe shi, shi ma a bakinsa. Sojojin sai suka fahimci ina ciki, kuma sun fi mutum dari a kewaye da dakin da nake ciki, sai suka yi ta ce min na fito. Kai da suka dame ni, da karfi na ce musu ba zan fito ba! Ni
duk damuwata su yi min luguden wuta ni ma, kamar yadda suka yi wa daya Haris din. Don da su kama ni ko na yi saranda, gaskiya gara sun harbe ni. Muna haka, can sai na ji wuta na cin daki, yana ta kokarin ya kona ni da raina. Sai na ji da wuta ta kona ni da raina gara dai na yi wani kokari ko da bindiga za ta fi mani saukin shahada.
Can sai na shiga wani daki da ke gaban wannan dakin. Shi ma dayan wanda suka harbe shi a bakin nan, sai ya yi kokarin fita, to shi sai suka ji motsinsa daman ba su gan shi ba; to sun dauka nune, sai suka sake masa ruwan wuta. Kawai nan take dai shi ma ya yi shahada a kan idona. Sai na dawo dakin da aka ajiye shahidan da 'yan daba suka kashe a Gabari. Nan dakin ma akwai shahidai masu yawa sosai, sai na shiga na rufe kaina kamar ni ma na yi shahada. A lokacin da na shiga na kwanta a cikin gawawwakin, a lokacin sojojin sun kama kowa, sun kashe na kashewa. Ba su yi tsammanin kuma akwai wata halitta da ke cikin Husainiyya mai numfashi ba. Allah dai ya sa kwanana na gaba. Duk abubuwan da suka rika yi a lokacin ina kallon su, domin duk sun farfasa wasu gine-ginen, kana iya kallon waje daga cikin dakin.
Tags
Zaria Massacre