Offline

MUZAHARAR ALLAH WADAI DA KISAN AL'UMMAR AREWA DAKUMA AL'UMMAR YEMEN YAU JUMA'A A ABUJA



- 18 February/ 16 Rajab.

'Yan uwa musulmi Almajiran Sayyid Zakzaky (h) sun gudanarda tagwayen muzaharori yau a babban birnin tarayyar Najeriya Abuja.

Dafarko dai 'yan uwan sunfara gabatarda muzaharar farkone a babban masallacin tarayyar Najeriya (Central Mosque Abuja), wannan muzaharar anyita ne domin nuna rashin amincewa da kisan Al'ummar kasar Yemen wanda saudiyya da kawayenta ke jagoranta tsawon shekaru.

Muzahara ta biyu kuma 'yan uwan sunyitane  domin nuna rashin amincewa da kisan Al'ummar arewacin Najeriya da akeyi da sunan 'yan bindiga a jahohin katsina,Zamfara,Sokoto dasauran jahohinda ake wannan kashe-kashe, angudanarda wannan muzahara ne a Area1 dake birnin tarayya Abuja.

Anyi dukkanin wadannan muzaharori lafiya, antashi lafiya.

© Freedom Fighters Ng.

Post a Comment

Previous Post Next Post