Da farko muna godiya ga Allah Ta’ala da ya raya mu, ya nuna mana wannan wata mai albarka da kuma daraja.Watan Rajab yana daga cikin watanni masu ayyuka na ibadodi da yawa,idan mutum ya yi bincike ma zai ga cewa baya ga watan Ramadan to babu watan da ya kai watan Rajab ibadodi masu yawa.Saboda haka yana da gayar muhimmanci ko wannenmu yayi amfani da wannan dama da kuma fursa zahabiyya domin ribatar wannan wata mai albarka,wato ta hanyar tsayuwa da ibadodin dake cikinsa.
- Ibadodin watan Rajab sun kasu kashi biyu:
1- Akwai ibadodi amma; Ibadodi amma sune ibadodin da ake so mutum ya aikata ko wane dare,ko kuma ko wace rana na watan Rajab.
2- Ibadodi kassa; Ibadodi kassa sune ibadodin da ake so mutum ya aikata a wasu kebantattun darare ko ranaku na watan Rajab,misali daren farko da kuma ranar farko,ko daren 15 da kuma ranar 15.ko daren 27 da kuma ranar 27 da dai sauransu.Wadannan ibadodi a dunkule sune: 1-Azumi.2-Salloli.3-Karatun Alkur’ani.4-Azkar.5-Addu’oi.6-Ziyara.7-Wanka.8-Umara.9-Sadaka.10-Nisantar zunubai.11-Ayyukan Ummi Dawuda.12-Raya darare. da dai sauransu.Insha Allah dai dai gwargwadon iko za a yi bayani kan ko wane daya daga cikinsu.
1-Azumi:Watan Rajab babban aikin ibada da ya shahara da shi a sunna da shia shine azumi,wato in mutum ya bincika a littafai zai ga cewa akwai ruwayoyi na hadisai masu yawa da suka zo ta mahangar shia da sunna kan falalolin azumtar watan Rajab,misali idan mutum ya duba cikin littafin Ikbal na Sayyid ibn dawus zai ga cewa ko wace rana daga cikin ranakun watan Rajab tun daga farkonsa har karshensa to akwai falalar azumin ranar.Saboda ma irin wadannan falaloli zamu ga bayin Allah masu yawa,sukan azumci watan ne baki dayansa.Kuma ko a wannan nahiya tamu in mutum ya duba zai ga cewa mutanenmu,musamman ma tsofaffi su kan azumci watan baki daya,har ma suna yi ma watan lakabi da watan azumin tsofaffi.Saboda haka ko da mutum ba zai iya azumtar watan Rajab din baki daya ba,to yana da gayar muhimmanci ya azumci akalla wasu muhimman ranaku na watan, misali ya azumci ranar farko,da ranar 13,14 ,15 da kuma ranar 27.
2-Salloli:Sallolin nafila da ke cikin wannan wata sun kasu kashi biyu,akwai salloli amma da kuma salloli kassa.Salloli amma sune sallolin da ake yin su a kowane dare daga cikin dararen watan Rajab.Idan mutum ya duba cikin littafin Diyaus-salihin ko littafin Ikbal ko littafin Baladul Amin zai ga an kawo nau’in sallar ko wane dare.Saboda haka yana da muhimmanci mutum yayi mujahada wajen ganin cewa salloli baki daya na dararen watan Rajab ya yi su,wato ba tare da ya rasa ko da dare guda ba.Salloli kassa na watan Rajab sune salloli na nafila da ake yi a wasu kebantattun darare ko ranaku na watan kamar sallolin daren farko ko ranar farko,ko sallolin daren 13,14,15 ko daren 27 da dai sauransu.Ga mai bukatar ganin irin wadannan salloli na kassa yana iya duba littafin Mafatihul jinan da yake ya kawo su,salloli na amma ne na watan Rajab bai samu kawowa ba.Ko da mutum bai samu iya tsayuwa da wadancan salloli na amma ba,to akalla ya tsayu da salloli na kassa,amma abun da yafi shine ya ga cewa ya aikata dukkansu wato sallolin amma din da kuma kassa domin ko wace daga cikin su tana da falaloli masu yawa.
3-Karatun Alkur’ani:Akwai wasu surori na Alkur’ani da suka zo a ruwayoyi na hadisi cewa ana son karanta su a kowane dare da kuma ko wace rana na watan Rajab.Wadannan surori ko sune:An ruwaito daga Imam Ali[AS] yace,Manzon Allah[S] yace, “Duk wanda ya karanta a kowane dare da kuma kowace rana surar Fatiha,da Ayatul kursiyyu,da kulya-ayyuhal-kafirun,da kul-huwallahu,da kul'auzu birabbil falak da kuma kul'auzu birabbin nas to Allah zai gafarta masa zunubansa baki daya.Ko wace sura mutum zai biya sau ukku ne.Haka nan ana son mutum ya karanta kul huwallahu sau dubu a watan Rajab,in kuma ba zai iya ba to akalla duk ranar Jumma’a na watan Rajab ya biya ta sau dari.Yazo a ruwaya cewa duk wanda ya aikata haka to zai kasance yana da wani haske ranar kiyama wanda zai jashi zuwa Aljanna.Saannan baya ga haka kuma ana son mutum ya yawaita karatun Alkur’ani a wannan wata na Rajab,wato dai ya samu ya sauke Alkur’ani da yawa,misali ya samu ya yi sauka goma ko bakwai ko biyar ko ukku in zai iya,in haka bai samu ba to akalla ya samu ya sauke Alkur’ani sau daya a cikin watan.
4-Azkar:Akwai wasu zikirori da suka zo a ruwayoyi ana son yinsu a watan Rajab,misali ana son fadin La’ilaha ilallah sau dubu ko wane dare.Manzon Allah[S] yace wanda yayi haka to za a rubuta masa lada dubu dari.Haka nan ana son mutum yace safe da yamma, “Astagfirullah wa a tubu ilaihi.Sau 70 idan ya kai 70 sai ya kammala da cewa Allahummag firli wa tub alayya.Da dai sauran wasu Azkar ana iya dubawa cikin littafin Mafatihul Jinan.
5-Addu’oi:Akwai addu’oi masu yawa da aka ruwaito daga Manzon Allah[S] da kuma Aimma[AS] da ake son karanta su a watan Rajab.Wa]ansu addu’oin amma ne,wato ko wace rana ake biya su a cikin watan.Wadansu addu’oin kuma kassa ne,wato wasu ranaku ne ko darare kebantattu a watan ake karanta su.Akwai kuma wata addu’ar ana son karantata bayan ko wace sallah ta wajibi,da kuma safe da yamma.Ga mai bukatar ganin wadannan addu’oi yana iya duba Mafatihu ko Ikbal da makamantansu.Wani tanbihi anan shine yana da gayar muhimmanci wadannan addu’oi na amma da kuma kassa na watan Rajab mutum ya kasance yayi su baki daya,domin yin haka tabbas zai yi tasiri ga Ruhin mutum,wato dai abincin ruhi ne.
6-Ziyara:Wannan wata na Rajab yana daga cikin watannin da ake son ziyarar Imam Ali[AS] Imam Husain[AS] da kuma Imam Rida[AS].Wannan Ziyara imma daga kusa ko nesa,wato in mutum na da ikon zuwa Najaf ko Karbala ko kuma Mash-had domin yin Ziyarar haka aka fi so,idan kuma mutum bai samu ikon zuwa ba,sai yayi ziyarar daga in da yake.Ranakun da ake wannan ziyara a cikin watan sune:Ziyarar Imam Husain[AS] a daren farko da kuma ranar farko,haka nan da daren 15 da kuma ranar 15.Sai kuma Ziyarar Amiril Muminin[AS] a ranar mab’as da kuma daren,wato daren 27 da kuma ranar.Haka nan ana son ziyarar Manzon Allah[S] daga kusa ko nesa a wannan rana ta 27.Dukkan wadannan ziyarori ko wannen su yana da falaloli masu yawa.
7-Wanka:Akwai wasu ranaku da kuma darare a cikin wannan wata na Rajab da ake son yin wanka a cikinsu,wato shigen wankan Jumma’a,wadannan ranaku da darare ko sune:Daren farko da ranar farko,daren 15 da ranar 15,daren 27 da kuma ranar 27,da daren karshe da kuma ranar.Manzon Allah[S] yace, “Duk wanda ya shiga watan Rajab ya yi wanka a farkonsa da tsakiyarsa da kuma karshensa,to zai tsarkaka daga zunubai kamar ranar da mahaifiyarsa ta haife shi.”Irin wadannan wanka da suka zo a ruwayoyi na hadisai da ake son yi a wasu lokuta na musamman,yana da gayar muhimmanci mutum ya lizimci yin su.Domin suna da tasiri wajen tazkiyyar naf’s dinsa.
8-Umra:Wannan wata na Rajab idan mutum na da iko,ana son mutum yayi aikin Umara a ciki,wato kamar yadda Imam Sajjad[AS] ya kasance yana yi.An ruwaito cewa Imam Aliy Zainul Abidin[AS] yayi Umara a wata na Rajab,kuma ya kasance yana yawaita Ibada a wadannan lokuta.A takaice dai yin Umara a watan Rajab ga wanda yake da ikon yi yana da falaloli masu yawa.
9-Sadaka:Daga cikin ayyuka na ibadodi da ake son yawaita yinsu a watan Rajab akwai sadaka.Yama zo cewa idan mutum bai da ikon azumtar wadannan ranaku na watan Rajab to ya yawaita yin sadakoki da kuma kyatuttuka.
10-Nisantar Zunubai:Aiki ko ibada babba kuma mafi girma da ake so mutum ya lizimta a watan Rajab shine nisantar zunubi,wato ya yi iyaka iyawarsa yaga cewa bai sa'a ma Allah Ta’ala ba a cikin wannan wata mai albarka.Domin wannan wata yana daya daga cikin watanni hudu masu alfarma wadanda aka hana zaluntar kai a cikinsu,to yana daga cikin zaluntar kai aikata zunubi.Kuma aikata zunubi yana da illoli masu yawa,daga cikinsu yana dabaibaiye mutum daga ayyukan ibada,misali akwai kissar wani bawan Allah,sakamakon ya munana ma wani zato ya kasa tashi sallar tahajjud.Saboda haka duk lokacin da mutum ya saba aikata wani aiki na ibada ko da’a,sai ya zamanto yanzu bai yi,to lalle ba mamaki ya aikata wani zunubi ko zunubai da suka shiga tsakaninsa da aikatawa.Akwai wanda yazo wajen Imam Ali[AS] yace masa,ya kasance kullum ya kan kwanta da nufin tashi yin sallar dare,amma kuma bai tashi,sai Imam Ali[AS] yace masa, “Zunubai ne suka dabaibaye shi.”
11-Ayyukan Ummi Dawuda:Daga cikin ayyukan ibadodi na watan Rajab akwai na Ummi Dawuda.kissar Ummi Dawuda da yadda ake wannan ibada da kuma fa’idodinta yana bukatar bayani ko da a takaice.Da farko Ummi Dawuda wata baiwar Allah ce da ta yi zamani da Imam Sadik [AS] a Sali shi ya bata wadannan ayyuka na ibada.Dauda danta ne,ainihin sunanta Fadima,to shi wannan Dawuda nasabarsa tana tukewa ga Imam Hassan[AS] ne.Wata waki’a ce ta faru a lokacin gashi Dawud,wanda ya kai ga mahaifiyarsa ta kai kukanta ga Imam Sadi}[AS] saboda ya taimaka mata da addu’a,to shine ya bata wadannan ayyuka,ikon Allah tana yinsu sai wannan matsala ta koranye.Abinda ya faru shine:Khalifan Abbasawa mai suna Mansur a lokacin yasa aka kama wasu daga cikin zuriyyar Sayyida Fadima [AS] daga Madina yasa akawo su Irak,da aka kawo su yasa aka tsare su a kurkuku.Bayan lokaci mai tsawo sai labarurruka dabam dabam suka dunga zuwa ma ita mahaifiyar Dawuda,wani lokaci labari yazo akan an kashe shi,wani lokaci kuma labari ya zo mata akan yana raye.Sai wata rana ta ji cewa Imam Sadik [AS] bai da lafiya,sai ta je ta gaishe shi,lokacin da ta tashi zata dawo gida sai Imam Sadik [AS] yace mata ya labarin Dawuda ne? tana jin sunan Dawuda sai ta fashe da kuka.Ta ce ya shugaba na yana kurkuku a Iraki,na debe tsammanin zamu sake haduwa.Ina so ka taimaka mani da addu’a kan al’amarinsa.To shine Imam Sadik yace mata idan watan Rajab ya kama ta azumci 13,14 da 15. To a ranar 15 shine Imam Sadik [AS] ya fa]a mata wasu surori da kuma addo’oi da zata yi.Tana yinsu ba a da]e ba,sai gashi an sako wannan da nata Dawud.Domin karin bayani kan wannan ayyuka na ummi Dawuda ana iya duba littafin Zadul Maad na Allama Majlisi,saboda ya kawo bayanan da sauran littafai basu kawo ba.Wani tambihi anan shine Ummi Dawuda ta tambayi Imam Sadik [AS] cewa,zata iya yin wadannan ayyuka ba a watan Rajab ba? Yace mata zata iya yi,misali wata bukata ta taso ma mutum ko matsaloli a wani wata cikin watanni,to sai ya azumci 13,14 da 15 na watan,bayan haka yayi wadannan addu’oi,to insha Allah zai samu biyan bukata da kuma warwaren matsaloli,domin wannan addu’a ta Ummi Dawuda tana da tasiri babba wajen yaye matsaloli da kuma biyan bukata.Bayin Allah masu yawa sun jarraba kuma sun samu biyan bukata.
12-Raya wasu darare:Akwai hadisai da suka zo dake bayanin falalar raya wasu darare na cikin watan Rajab,misali daren farko da kuma daren 15 da kuma daren 27.Saboda haka yana da muhimmanci mutum yayi mujahada wajen ganin cewa ya raya wadannan darare masu albarka da ibadodi.Akwai darare da ake son mutum idan zai iya ya lizimci raya su misali duk daren jumma’a,dararen watan Ramadan baki dayansu da dai sauransa,domin yin haka yana da falala da albarka mai yawa.
©Copyright: Muhammad Sulaiman Kaduna (Tambihi)
Tags
A'amal