Offline

Abubuwan Da Suka Faru A Rajab


Abubuwa da Ranakunda suka faru

_ Haihuwar Imam Muhamad al-Bakir (a.s)
1 Ga Watan Rajab

_ Shahadar Imam Ali an-Hadi (a.s)
3 Ga Watan Rajab

_ Haihuwar Imam Muhammad al-Jawad (a.s) 10 Ga Watan Rajab

_ Haihuwar Imam Ali Ibn Abi Talib (a.s) 13 Ga Watan Rajab

_ Shahadar Sayyida Zainab (a.s)
15 Ga Watan Rajab

_ Shahadar Imam Musa al-Kadhim (a.s) 25 Ga Watan Rajab

_ Shahadar Sayyiduna Abu Talib (a.s) 26 Ga Watan Rajab

_ Mi'irajin Manzon Allah (S) 27 Ga Watan Rajab
 

Falala da Ayyukan Rajab

Falala da Wasu Daga Cikin Ayyukan Da Ake Son Aikatawa a Wannan Wata.
Wannan wata na Rajab da Sha'aban da Ramalana watanni ne da suke da girma da kuma falaloli masu yawan gaske.

An ruwaito Manzon Allah (s) yana cewa:

rajab wata ne na Ubangiji mai girma, wani wata daga cikin watanni bai yi kusa da shi ba wajen falala da daukaka, Yakan kafirai a cikinsa haramun ne. Ku sani fa Rajab wata ne na Allah Madaukakin Sarki, watan Sha'aban kuwa wata na ne, sannan Ramalana kuwa watan al'ummata ne; ku sani duk wanda ya azumci rana guda cikin wannan wata zai samu yardar Allah da kuma nesanta shi daga fushin Allah da kuma rufe masa kofa daga cikin kofofin wuta.

Haka nan kuma an ruwaito Imam Musa bn Ja'afar (a.s) yana cewa:

Wanda ya azumci rana guda cikin wannan wata na Rajab, za a nesanta shi da wuta kimanin tafiyar shekara guda, wanda kuwa ya azumce shi na kwanaki uku, to za a sanya shi a Aljanna.

Haka nan kuma an ruwaito daga gare shi (a.s) cewa:

Rajab wani kogi ne daga cikin Aljanna, farinsa ya fi nono haka nan kuma zakinsa ya fi zuma; duk wanda ya azumci rana guda daga cikinsa, Allah Madaukakin Sarki Zai shayar da shi daga wannan kogi.

Har ila yau an ruwaito Imam Ja'afar al-Sadik (a.s) yana cewa:

Manzon Allah (s) yana cewa: Rajab wata ne na neman gafarar Ubangiji ga al'ummata, don haka ku yawaita yin istigfari a cikinsa, don kuwa Allah Mai gafara ne, Kuma Mai Rahama....Ku yawaita fadin: Astagfirullah Wa Asluhuttaubah.

Wannan wata dai yana da falaloli da yawan gaske, mai son karin bayani sai ya koma littattafan da suka yi magana kan hakan.

Sannan kuma an ruwaito cewa duk wanda ba zai iya yin wadannan abubuwa da muka ambata ba, to yana iya karanta wannan tasbihi sau dari kowace rana don ya samu ladan masu azumin. Tasbihin kuwa shi ne:

Subhana Ilalahil Jalili; Subhana Man La Yanbagi al-Tasbihu Illa Lahu, Subhana al-A'azzi al-Akram, Subhana Man Labisa al-Izza wa Huwa Lahu Ahlun

Haka nan kuma bayan azumi a cikin wannan wata akwai wata salla kuma da Manzon Allah (s) ya kwadaitar da mu da mu yi a ranar Alhamis na farko na wannan wata mai alfarma wanda ya ce duk wanda ya yi ta zai samu wadannan falaloli:
 
Gafarar manyan zunubai.
Garkuwa daga bala'in daren farko cikin kabari, da kuma samun matsuguni a Ranar Hisabi, bayan an hura kaho. Wannan salla za ta zo kabarin wanda ya aikatata cikin mafi kyawun yanayi tana mai cewa: "Ya masoyina, ina maka albishir da tsira daga dukkan wahalhalu. Mutum zai tambaya: 'Wane ne kai, don ban taba ganin fuska mai kyau kamar taka ba, kuma ban taba jin magana mai dadi kamar taka ba, kamar yadda kuma ban taba jin kamshin mai dadi irin kamshinka ba?. Sai sallar ta ce masa: 'Ya Masoyina! Nine ladan sallar nan da ka yi a daren kaza, a gari kaza, a wata na kaza kana kuma a shekara ta kaza. Na zo cikin wannan dare ne don saka maka da kuma cire maka duk wata damuwa ta kadaitaka da rashin sanin makoma da kake ciki. Kuma lokacin da za a hura kaho zan kasance maka inuwa a kanka. Don haka ka kasance cikin farin ciki Kuma babu abin da za a rage maka har abada'.

Yadda Ake Yin Sallar:

Da farko dai ka yi azumi a wannan ranar Alhamis ta farko na rajab, lokacin da ka zo sallar magariba da lisha, tsakanin wadannan salloli biyu sai ka yi raka'oi goma sha biyu, kana mai yin sallama bayan kowani raka'oi biyu. A kowace raka'a za ka karanta Suratul Fatiha sau guda da kuma Inna Anzalnahu sau sau uku da kuma Kulhuwallahu Ahadun sau goma sha biyu.

Bayan ka idar da wannan salla sai kuma ka karanta, wannan addu'an ko kuma salati sau saba'in (70):
 
"Allahumma Salli `Ala Muhammad, Annabiyyil Ummiyyi, Wa `Ala Aalihi" Daga nan sai ka yi sujada ka karatan wannan du'a'i sau saba'in alhali kana cikin sujadan:
 
"Subbuhun Quddusun, Rabbul Mala`ikati Warruh". Daga sai ka dago kanka ka karanta wannan addu'a sau saba'in:
 
"Rabbigh-Fir, War-ham, Watajawaz `Amma Ta'alamu, Innaka antal `aliyyul A`a-zam" .
 
Daga nan sai ka roki abin da kake so, Allah Zai biya maka bukatanka Inshallah.

Copyright; Muhammad Auwal Bauchi

Post a Comment

Previous Post Next Post