"A yan shekarun baya naji ance an daga takalmi, wanda Nelson Mandela yayi amfani dashi lokacin yana kurkuku, Nelson Mandela ya shafe shekaru ishirin da bakwai a kurkuku yana fufutukan nemawa yan uwansa bakar fata ta Afirika ta kudu yanci, saboda haka ya zamu gwarzo na mutanensa harma sauran mutane suke kallonshi a matsayin gwarzo, toh takalmi da ya taka yasa yana kurkuku sai gashi an daga shi, an ce to wa zai siya? Sai wani ya ce dala 500, wani yace dala 1000, wani yace ya kara kaza, kama dai sai da anihin takalmi yakai dala dubu dari, wanda anan in aka maida dala dubu dari sau dari, nawa kenan? Naira miliyan daya, koh ? Toh kaga takalmi kenan na Mandela, yanzu da za'a ce ga takalmin manzon Allah, ace wa zai siya ? Toh ai ko da ance mu kawo jinainenmu ne, ko ba'a lura ba? Toh lallai kam, ace in mun cika duro dinnan da jininmu za'a bamu takalmin nan zamuyi, don burinmu shine, da shina iya yiwuwa a maishe mu kasa takalmin manzon Allah ya taka, toh da zamu ga cewa mun sami daraja."
SAYYID ZAKZAKY (H) A WANI JAWABI MAI TAKEN SON ANNABI WAJIBI NE
Tags
Shaikh Zakzaky