Kasancewar wannan maudu'i mai matukar tsauri musamman yanzu da aka siyasantar da addini zuwa maslahar wasu mutane, amma abu ne mai kyau musulmi ya wadatu da sani akan muhimman al'amuran da suka wakana kafin da lokacin wafatin Mawlatiy Zahra salamullahi alaiha. Saboda saɓanin da ake dashi tsakanin Makarantu biyu na Musulunci, ina nufin sunnah da shia, zan kawo hujjoji daga dukkan bangarori, a karshe kuma sai mu bar wa mai karatu cikakkiyar dama ya zabi fahimtar da tafi gamsar dashi.
Yan shi'a sun tafi akan cewa Wafatin Nana Faɗima ya biyo bayan wasu nau'ikan cin zarafi da ta fuskanta a bayan wafatin Manzon Allah SAWA.
Suna kafa hujja da Hadisin da aka ruwaito daga Nana A'isha Bint Abubakar Bn Abi Ƙuhafa cewa, Sayyida Faɗima SA ta nemi Khalifa Abubakar bn Abi Ƙuhafa ya bata abubuwa guda 3, sune Gadon ta, Fadak, da kuma Khumusi. Sai Khalifa yace da ita Annabi SAWA yace ba a'a gadon mu, abinda muka bari sadaka ne. Wannan yasa Khalifa Abubakar ya hana Sayyida Faɗima duka abunuwa ukun da ta buƙata.
Wannan al'amari ya sanya Sayyida Faɗima fushi da Khalifa Abubakar, sanadin haka ta kaurace masa, bata sake yi masa magana ba har tayi wafati watanni shida bayan wafatin Mahaifin Ta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallam.
Lokacin da Sayyida Faɗima SA tayi shahada, Imam Ali AS ya binne ta da daddare, bai gayyaci Khalifa Abubakar ba don yi mata jana'iza, Imam Ali ne ya mata sallar Jana'iza.
Hadisin Nana A'isha da na ambata a sama ba wai iya a littafan shia yazo ba, ya zo har cikin Littafan Ahlussunnah da ake kira ''Sahihul Bukhari'' da ''Sahihu Muslim''. Ga matanin hadisin nan a kasa;
حَدَّثَنِي مُحَمَّدُ بْنُ رَافِعٍ، أَخْبَرَنَا حُجَيْنٌ، حَدَّثَنَا لَيْثٌ، عَنْ عُقَيْلٍ، عَنِ ابْنِ شِهَابٍ، عَنْ عُرْوَةَ بْنِ الزُّبَيْرِ، عَنْ عَائِشَةَ، أَنَّهَا أَخْبَرَتْهُ، أَنَّ فَاطِمَةَ بِنْتَ رَسُولِ اللَّهِ(ص)َ أَرْسَلَتْ إِلَى أَبِي بَكْرٍ الصِّدِّيقِ تَسْأَلُهُ مِيرَاثَهَا مِنْ رَسُولِ اللَّهِ(ص)َ مِمَّا أَفَاءَ اللَّهُ عَلَيْهِ بِالْمَدِينَةِ، وَفَدَكٍ، وَمَا بَقِيَ مِنْ خُمْسِ خَيْبَرَ، فَقَالَ أَبُو بَكْرٍ : إِنَّ رَسُولَ اللَّهِ(صَ) قَالَ: "لَا نُورَثُ، مَا تَرَكْنَا صَدَقَةٌ".... فَأَبَى أَبُو بَكْرٍ أَنْ يَدْفَعَ إِلَى فَاطِمَةَ شَيْئًا، فَوَجَدَتْ فَاطِمَةُ عَلَى أَبِي بَكْرٍ فِي ذَلِكَ، قَالَ: فَهَجَرَتْهُ، فَلَمْ تُكَلِّمْهُ حَتَّى تُوُفِّيَتْ وَعَاشَتْ بَعْدَ رَسُولِ اللَّهِ(صَ) سِتَّةَ أَشْهُرٍ، فَلَمَّا تُوُفِّيَتْ دَفَنَهَا زَوْجُهَا عَلِيُّ بْنُ أَبِي طَالِبٍ لَيْلًا، وَلَمْ يُؤْذِنْ بِهَا أَبَا بَكْرٍ، وَصَلَّى عَلَيْهَا عَلِيٌّ...
Bukhari hadisi mai lamba 3092, 3094, 3711, 4033, 4035, 4240, 5358, 6725, 6728, 6730, 7305 ).
- صحيح مسلم كتاب : الجهاد والسير | باب : قول النبي : "لا نورث، ما تركنا فهو صدقة"، الجزء رقم : 5، الصفحة رقم :153، الحديث : 1759 ( 52 )، 1757, 1758, 1759.
Bayan su akwai wasu littattafan Ahlussunnah kamar haka:
سنن أبي داود
( 2963, 2968, 2976 ).
سنن الترمذي
( 1608, 1609, 1610 ).
سنن النسائي
( 4141 )
موطأ مالك
( 2840 ).
مسند أحمد
(9, 25, 55, 58, 60, 78, 79, 425, 1781, 1782, 25125, 26260 ).
Nana Faɗima ta dogara da Alqur'ani a matsayin hujjar ta kan neman gadon mahaifin ta, wanda a har zuwa yau mabiya shi'a da wasu daga ahlussunnah suna ganin cewa lallai fahimtar Nana Faɗima itace gaskiya kuma itace daidai, Nima fahimta ta kenan. Allahu A'alamu.
Yan shia suna kawo cewa kafin wafatin ta salamullahi alaiha, bayan hana ta gado, Fadak da kuma Khumusi da Khalifa Abubakar yayi, sun kawo cewa yayi umarni a je a bincike gidan ta ko akwai dukiyar Allah da Nana Faɗima ta ajiye a gidan a fito da ita.
Babban malamin Ahlussunnah sheikhul Islam Ibn Taimiyya ya tabbatar da haka a cikin littafin sa Minhajussunnah, Yake cewa:
ﻭَﻏَﺎﻳَﺔُ ﻣَﺎ ﻳُﻘَﺎﻝُ : ﺇِﻧَّﻪُ ﻛﺒﺲ ﺍﻟْﺒَﻴْﺖَ ﻟِﻴَﻨْﻈُﺮَ ﻫَﻞْ ﻓِﻴﻪِ ﺷَﻲْﺀٌ ﻣِﻦْ ﻣَﺎﻝِ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﺍﻟَّﺬِﻱ ﻳُﻘَﺴِّﻤُﻪُ، ﻭَﺃَﻥْ ﻳُﻌْﻄِﻴَﻪُ ﻟِﻤُﺴْﺘَﺤِﻘِّﻪِ، ﺛُﻢَّ ﺭَﺃَﻯ ﺃَﻧَّﻪُ ﻟَﻮْ ﺗَﺮَﻛَﻪُ ﻟَﻬُﻢْ ﻟَﺠَﺎﺯَ؛ ﻓَﺈِﻧَّﻪُ ﻳَﺠُﻮﺯُ ﺃَﻥْ ﻳُﻌْﻄِﻴَﻬُﻢْ ﻣِﻦْ ﻣَﺎﻝِ ﺍﻟْﻔَﻲْﺀِ .
- ﻣﻨﻬﺎﺝ ﺍﻟﺴﻨﺔ ﺍﻟﻨﺒﻮﻳﺔ ﻓﻲ ﻧﻘﺾ ﻛﻼﻡ ﺍﻟﺸﻴﻌﺔ ﺍﻟﻘﺪﺭﻳﺔ : ﺍﺑﻦ ﺗﻴﻤﻴﺔ : ﺝ 8 ، ﺹ 291
A wannan yunƙuri da akai na bincike a gidan Nana Faɗinsa SA, an ruwaito cewa Khalifa Umar Bin Khattab ya bigi Sayyida Zahra salamullahi alaiha a ciki wanda shine yayi sanadiyar ɓari da tayi na cikin Muhsin, Sannan kuma aka ruwaito cewa Khalifa Umar cikin fushi yayi umarnin a ƙone gidan da duk wanda ke cikin sa, ciki har da Imam Hassan da Imam Hussaini SA.
Wani Malamin Ahlussunnah mai suna Shahristani ya kawo cikin littafin sa kamar haka:
ﺍﻥ ﻋﻤﺮ ﺿﺮﺏ ﺑﻄﻦ ﻓﺎﻃﻤﺔ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﺒﻴﻌﺔ ﺣﺘﻰ ﺍﻟﻘﺖ ﺍﻟﺠﻨﻴﻦ ﻣﻦ ﺑﻄﻨﻬﺎ ﻭﻛﺎﻥ ﻳﺼﻴﺢ ﺍﺣﺮﻗﻮﺍ ﺩﺍﺭﻫﺎ ﺑﻤﻦ ﻓﻴﻬﺎ ﻭﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻓﻲ ﺍﻟﺪﺍﺭ ﻏﻴﺮ ﻋﻠﻰ ﻭﻓﺎﻃﻤﺔ ﻭﺍﻟﺤﺴﻦ ﻭﺍﻟﺤﺴﻴﻦ ...
- ﺍﻟﻤﻠﻞ ﻭﺍﻟﻨﺤﻞ : ﺍﻟﺸﻬﺮﺳﺘﺎﻧﻲ، ﺝ ١، ﺹ ٥٧ . ﺗﺎﺭﻳﺦ ﺍﻟﻮﻓﺎﺓ : ٥٤٨ . ﺗﺤﻘﻴﻖ : ﻣﺤﻤﺪ ﺳﻴﺪ ﻛﻴﻼﻧﻲ . ﺩﺍﺭ ﺍﻟﻤﻌﺮﻓﺔ، ﺑﻴﺮﻭﺕ - ﻟﺒﻨﺎﻥ .
Yan shia suna kan cewa Khalifa Abubakar da Khalifa Umar ba su tsaya akan tauye hakkin Fatimah (as) akan Khumusi, gadon babanta(saw) da Fadak ba kadai, sai da Umar ya jagoranci kona gidanta(as).
Akwai ruwaya daga Abubakar Ibn Abi Shaiba ( malamin Bukhari da Muslim) ya riwaito Khalifa Umar Ibn Khattab da kansa ya na gadarar zai kona gidan Az-Zahra(as):
حدثنا محمد بن بشر نا عبيد الله بن عمر حدثنا زيد بن أسلم عن أبيه أسلم أنه حين بويع لأبي بكر بعد رسول الله(ص) كان علي والزبير يدخلان على فاطمة بنت رسول الله(ص) فيشاورونها ويرتجعون في أمرهم، فلما بلغ ذلك عمر بن الخطاب خرج حتى دخل على فاطمة فقال: ...وأيم الله ما ذاك بمانعي إن اجتمع هؤلاء النفر عندك، إن أمرتهم أن يحرق عليهم البيت، قال: فلما خرج عمر جاؤوها فقالت: تعلمون أن عمر قد جاءني وقد حلف بالله لئن عدتم ليحرقن عليكم البيت...
- المصنف : ابن أبي شيبة الكوفي، ج ٨، ص ٥٧٢. تاريخ الوفاة : ٢٣٥. تحقيق : تحقيق وتعليق : سعيد اللحام. الطبعة : الأولى. تاريخ النشر : جماد الآخرة ١٤٠٩ - ١٩٨٩ م. مكتب الدراسات والبحوث في دار الفكر، دار الفكر.
Tabari shima ya riwaito Khalifa Umar Ibn Khattab ya kai harin kona gidan Az-Zahra(as) ne; alhali a gidan akwai Sahabbai Al-muhajirun, daga ciki har da Talha, Az-zubair, yace wallahi zai koma gidan da su ko su fito suyi mubaya'a.
حدثنا ابن حميد قال حدثنا جرير عن مغيرة عن زياد بن كليب قال أتى عمر بن الخطاب منزل علي وفيه طلحة والزبير ورجال من المهاجرين فقال والله لأحرقن عليكم أو لتخرجن إلى البيعة...
- تاريخ الطبري : الطبري، ج ٢، ص ٤٤٣. تاريخ الوفاة : ٣١٠. تحقيق : مراجعة وتصحيح وضبط : نخبة من العلماء الأجلاء. مؤسسة الأعلمي للمطبوعات، بيروت - لبنان.
Malam Al-yakubi shima ya nakalto cewa; lokacin da Khalifa Abubakar da Khalifa Umar su ka samu labarin wasu Sahabbai sun taru a gidan Imam Ali(as), sai Abubakar da Umar su ka zo da tawaga, su ka farmaki gidan Az-Zahra(as):
وبلغ أبا بكر وعمر أن جماعة من المهاجرين والأنصار قد اجتمعوا مع علي بن أبي طالب في منزل فاطمة بنت رسول الله، فأتوا في جماعة حتى هجموا الدار...
- تاريخ اليعقوبي : اليعقوبي، ج ٢، ص ١٢٦. تاريخ الوفاة : ٢٨٤. ناشر: مؤسسة ونشر فرهنگ أهل بيت(ع) - قم خيابان حجت صندوق پستى ١١ - تلفن ٢٧٣٤٨. دار صادر، بيروت.
Wadannan na daga hujjojin da yan shia suka dogara dasu wajen bayanin wafatin Nana Faɗima da alakar wafatin ta da abubuwan da suka wakana na ƙona gidan ta, hana ta gado da kuma bugun da akai mata har tayi ɓari.
Sukam ce shiyasa a lokacin wafatin khalifa Abubakar, ya yi nadamar wannan harin da ya kai gidan Nana Fadima SA. Tabari ya kawo cikin tarihin da kamar haka;
حدثنا أبو الزنباع روح بن الفرج المصري ثنا سعيد بن عفير حدثني علوان بن داود البجلي عن حميد بن عبد الرحمن بن حميد بن عبد الرحمن بن عوف عن صالح بن كيسان عن حميد بن عبد الرحمن بن عوف عن أبيه قال دخلت على أبي بكر(ر) أعوده في مرضه الذي توفي فيه... فقال... فوددت أني لم أكن كشفت بيت فاطمة وتركته وأن أغلق علي الحرب ووددت أني يوم سقيفة بني ساعدة كنت قذفت الامر في عنق أحد الرجلين أبي عبيدة أو عمر فكان أمير المؤمنين وكنت وزيرا...
- المعجم الكبير : الطبراني، ج ١، ص ٦٢. تاريخ الوفاة : ٣٦٠. تحقيق : تحقيق وتخريج : حمدي عبد المجيد السلفي. الطبعة : الثانية، مزيدة ومنقحة..
Wannan shine abinda na samu damar rairayo wa dan gane da wafatin Nana Faɗima daga makarantu 2 na Musulunci, sunnah da shi'a.
Allah ya kara tsira da aminci ga shugabar mu Faɗima yar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wa Alihi Wasallama.
Aliyu Samba
19/12/2021
Tags
Mourning Session