Yanzu lokaci ne da Kafircin duniya suka yiwa Musulmi kule, “kule din ga Musulmi ne. Yanzun Kafiricin duniya ya dana kibiya ya ce ma Musulmi Kule? Kulenku? To, me ya kamata mu ce masa? 'Ca-cas-cas-cas-cas! Ya kamata mu nuna masa karyanka! Musulunci sosai ga shi kuma zaka ganshi a jikinmu. To, lazim ne mutum ya yi addini, addinin nan ba magana bane kawai, imani ne da aiki! Dole ne mutum ya san meye ya hau kansa? Wajibin da ya hau kansa na addini kuma ya aikata a aikace. Idan ina aikatawa, kana aikatawa, kina aikatawa, aka samu ma’aikata, idan aka ganmu, za a ga addini ne.”
-Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) a jawabin Maulidin Manzon Allah da ya gudana a farkon wannan watan Rabi'ul Awwal a bakin Kasuwar cikin garin Zariya na shekarar 2015.
Tags
Shaikh Zakzaky