– Ma'aikatar harkokin wajen Iran ta jaddada cewa kisan Janar Qassem Soleimani harin ta'addanci ne wanda ya saba wa dokokin kasa da kasa kuma ko shakka babu gwamnatin Amurka ce ke da alhakin lamarin.
Ma'aikatar harkokin wajen Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fitar da sanarwa a jajibirin cika shekaru biyu da shahadar tsohon kwamandan rundunar Quds ta IRGC ta Iran Laftanar Janar Qassem Soleimani.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, shahidin Soleimani a ko da yaushe yana taka rawar da ya dace da manufofin jamhuriyar Musulunci ta Iran tare da taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a matakin shiyya-shiyya da na kasa da kasa.
Ya yi amfani da rayuwarsa wajen yaki da ta'addanci na kasa da kasa da kuma karuwar kungiyoyin ta'addanci a yankin, in ji sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, a wani mataki na laifi da ya saba wa dokokin kasa da kasa, Amurka takai harin ta'addanci kan daya daga cikin manyan jami'an Iran a kasar Iraki.
Kisan gillar da aka yi wa gwarazan yaki da ta'addanci na kasa da kasa ya bayyana ma'auni biyu na Amurka kuma sako ne na nuna goyon baya ga kungiyoyin 'yan ta'adda.
Babu shakka, laifin da Amurka ta aikata a kisan Janar Soleimani, misali ne na harin ta'addanci da gwamnatin Amurka ta yi ta shirya kuma a yanzu fadar White House ce ke da alhakin wannan lamarin.
Sojojin Amurka ne 'yan ta'adda sun kashe tsohon kwamandan Quds na IRGC na Iran Laftanar Janar Qassem Soleimani da kuma babban kwamandan rundunar hadin gwiwa ta Iraki (PMU) na biyu a kusa da filin jirgin sama na Iraki a ranar 3 ga Janairu, 2020, bisa umarnin tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump.
Mahadi Tukur Almizan.
_ Freedom Fighters Ng.
Tags
Resistance News